Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta damke wasu bata gari 26

Runduanar ‘yan sandan jihar Osun, ta kama kuma ta gabatarwa taron yan jarida wadansu masu aikata laifuffuka 26 da suka harda da masu sata da garkuwa da mutane, da masu fashi da makami da wadanda suka kware wajen satar motoci da babura da kuma wani wanda yayi shigar mata. Yace shi mace ce ta yanar gizo, har ya samu nasarar damfarar wani ba’amerke dala dubu 80.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun Mr. Femi Oyeleye ya gabatarwa ‘da yan jarida wadannan bata gari a birnin Oshogbo baban birnin jihar Osun.

Ya bayyana cewa wanda ya damfari ba’amerken ya gabatar da kansa a zaman mace ta yanar gizo, har ya samu nasarar dafarar baturen inda ya sanya masa kudi a asusu ajiyarsa na baki.

Kwamishinan ‘yan sanda yace irin wannan zamba ke bata sunan Nigeria a idon duniya.

2507total visits,1visits today


Karanta:  Gungun mutane sun kashe sojan Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.