Rundunar ‘Yan sandar Nigeria Ta Jaddada Cewa Beli Kyauta Ne

Rundubar ‘yan sandan Nigeria ta samar da wani gangamin wayar wa mutane da kai akan beli.Rundunar ta jadadda cewa beli kyauta ne don haka jama’a su kula.

Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta kaddamar da shirin wayar da kan jamaar kasa cewa beli kyauta ne.

Da yake kaddamar da shirin a Minna fadar gwamnatin jihar Niger, babban sufeto- janar na ‘yan sandan Nigeria, Ibrahim Idris yace zasu zagaye Nigeria kaf domin yinwannan yekuwar.

Yace mutane su kwana da sanin cewa beli a caji ofis kyauta ne, ba’a biyan ko sisi kwabo, don haka duk wanda ya bayar da wasu kudade da kuma wanda ya karba duk masu laifi ne.

Asalin Labari:

VOA Hausa

143total visits,1visits today


Karanta:  An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen 'yan sanda

Leave a Reply

Your email address will not be published.