Sabuwar Shekarar Musulunci: Jihar Kano Ta Sanar Da Hutun Aiki Ranar Jumma’a.

Daga Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta sanar cewa babu aiki ranar Jumma’a 22 ga watan Satumba don shaidawa da tsayawar sabuwar shekarar musulunci.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Malam Ibrahim Garba ya sakawa hannu ya kuma bawa manema labarai a Kano ranar Laraba.

Sabuwar Shekarar Musuluncin ta dace da ayyukan da aka saba gudanarwa na murnar samun ‘yancin kan kasa.

Garban ya ambato mukaddashin gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar na taya jama’r jihar dama duniya bakidaya murnar zagayowar shekarar

Yake cewa Abubakar na kira ga Kanawa dasu amfani hutun don gudanar da addu’o’in zaman lafiya da fatan alheri ga kasa bakidaya.
yakuma ce mukaddashin gwamnan ya kara jaddadawa jama’ar jihar burinsa na yin aiki tukuru don habaka yanayin zaman takewar rayuwarsu.
Ya kuma kara kiran ‘yan Nijeriya dasu hada hannu da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan burinta na samar da zaman lafiya da wanzar da jin dadin a kasa bakidaya.

Kamfanin Dillancin Labarai ya rawaito cewa ranar Jumma’a 22 ga watan Satumba shi ne daya ga watan Muharram, watan farko a kalandar musulunci kuma shi yake nuna farkon kamawar sabuwar shekara ta Hijra ta 1439. (NAN)

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

682total visits,2visits today


Karanta:  Kwankwaso ya Kauracewa Babban Taron APC a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.