An sake kai hari a Jami’ar Maiduguri

‘Yan kunar bakin wake sun tashi bama-baman da ke jikinsu a Jami’ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu da ma wata ma’aikaciyar Jami’ar.

Kakakin Jami’ar Farfesa Danjuma Gambo ya shaida wa BBC cewa maharan sun tashi bama-baman ne a wuri uku.

“Mace ta farko ta tunkari jami’an tsaron da ke aiki a jami’ar ne inda ta tayar da bam din da ke jikinta. Daya daga cikin jami’an tsaron ta mutu sannan an kai uku asibiti. Ta biyu kuma ta shigo ta gabashin Jami’ar amma jami’an tsaro suka gan ta, nan take suka harbe ta. Bam na uku kuma ya tashi ne a can nesa da jami’ar don haka ba mu sani ba ko mace ce ko namji suka yi yunkurin kai harin”.

Farfesa Gambo ya ce hukumomi na ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Jami’ar, yana mai cewa ana kai irin wadannan hare-hare ne saboda girman da Jami’ar ke da shi kuma ba a katange dukkanta ba.

A wannan shekarar dai an sha kai hare-haren kunar bakin wake a Jami’ar ta Maiduguri, abin da wasu ke ganin na da nasaba da rashin inganta tsaro a Jami’ar, ko da yake hukumomin tsaron na cewa suna yin bakin kokarinsu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

314total visits,1visits today


Karanta:  Mene ne Shugaba Buhari Bai Fada Ba a Jawabinsa?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.