Salah ya koma Liverpool a kan fam miliyan 34

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta kammala cinikin dan wasan Roma Mohamed Salah a kan fam miliyan 34.

Dan kasar Masar, Salah mai shekara 25 da haihuwa, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ne da Liverpool.

A shekarar 2014 dan wasan ya so ya koma Liverpool, amma sai ya koma kulob din Chelsea.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana jin dadinsa game da sayen dan wasan.

Ya ce: “Salah yana da gogewa sosai kuma abin farin ciki ne da ya yarda ya kasance tare da mu.”

Salah zai rika sanya rigar mai lamba 11 ne yayin da Roberto Firmino zai koma sanya mai lamba tara.

Salah ya taka muhimmiyar rawa a kakar Serie A ta bara a Roma, inda kungiyar ta kammala gasar a mataki na biyu.

Kuma ya buga wasa 31 ne, ya zura kwallaye 15 a raga.

Asalin Labari:

BBC Hausa

448total visits,1visits today


Karanta:  Arsenal za ta buga Europa bayan shekara 20

Leave a Reply

Your email address will not be published.