Sanatocin Amurka sun soki Twitter

An soki kamfanin shafin Twitter saboda ‘yar takaitacciyar bayyana wadda ba ta wadatar ba, da wakilansa suka yi a gaban kwamitin da ke binciken katsa-landan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata.

An gayyaci jami’an kamfanin na Twitter da su bayyana domin su bayar da bahasin da suke da shi na amfani da shafin wajen yada bayanan karya ga masu zaben Amurka.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron ganawar da jami’an kamfanin, dan majalisar dattawan Amurka, Mark Warner, ya bayyana bahasin da wakilan shafin suka bayar a matsayin babban abin takaici.

Ya zargi kamfanin da kin fahimtar muhimmancin lamarin, ta yadda kawai ya maimaita irin bayanan da masu shafin Facebook suka ba wa kwamitin.

Shi dai Sanata Warner yana fafutukar ganin an sanya wa kamfanonin fasaha ne tsauraran matakai kan ayyukansu, musamman ma a kan saba dokokin tallace-tallace ta intanet.

A wani sako da shafin Twitter ya wallafa ranar Alhamis, ya ce, kafar watsa labarai ta Russia Today, wadda ke da alaka ta kut da kut da fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta kashe dala dubu 274, wajen tallace-tallace a lokacin yakin neman zaben na Amurka.

Shafin na Twitter ya kuma ce ya gano tare da dakatar da shafuka daban-daban har 22 da ake amfani da su wajen yada bayanai da sakonni na karya.

Shi dai shafin Twitter kusan ya zama dandali da shugaba Donald Trump, wanda ake zargin kutsen da Rasha ta yi a zaben dominsa, amfani da shi akai akai wajen watsa maganganunsa.

Hakan ne ma ya sa har ta kai an bukaci shafin da ya bayar da bayani kan dalilin da ya sa ba ya ganin rubuce-rubucen da Mista Trump ke yi a cikinsa ba su saba ka’idarsa ba.

Karanta:  An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

Rubutun da ya jawo wannan magana kuwa shi ne, wanda Shugaban yake barazana ga Koriya ta Arewa, cewa zai tarwatsa kasar.

Mutane da dama na ganin rubutun ya saba ka’idojin shafin, wadanda suka haramta yin barazanar ta’addanci, a don haka ya kamata a cire rubutun.

To amma a martanin da kamfanin shafin ya mayar ya ce ya bar rubutun ne saboda labari ne mai muhimmanci.

Kuma kamfanin ya ce yana la’akari da muhimmancin rubutu kafin ya yanke hukuncin barinsa ko kuma cire shi, ko da kuwa ana ganin ya saba wa ka’ida.

Asalin Labari:

BBC Hausa

3514total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.