Sarauniyar Ingila ta nada dan Ghana a matsayin hadiminta

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu ta nada wani dan Ghana a matsayin babban hadiminta wanda zai rika taimakawa wajen kula da harkokin fadarta.

Major Nana Kofi Twumasi-Ankrah wanda soja ne da aka haife shi a kasar Ghana.

Ya je Birtaniya ne tare da iyayensa a shekarar 1982.

Ya yi karatu ne a jami’ar Queen Mary University da ke Landan da kuma makarantar sojoji ta Royal Military Academy Sandhurst.

Tun bayan da ya samu horo a makarantar ne ya zama sojan Birtaniya bakar fata na farko da aka nada dogarin fadar sauraniyar.

Mista Twumasi-Ankrah ya yi aikin samar da tsaro lokacin daurin auren Yarima William da Kate Middleton a shekarar 2011 da kuma wani faretin walimar da aka shirya wa Sarauniyar.

A nan gaba kadan ne zai fara sabon aikin da aka nada shi bayan karewar wa’adin wanda zai maye gurbinsa.

Ana daukar kwararrun mutane don su yi aiki a fadar ba tare da la’akari da jinsi ko launin fata ko kuma addininsu ba, kamar yadda dokokin tafiyar da fadar sarauniyar suka zayyana.

Mista Twumasi-Ankrah yana da mata da ‘ya’ya mata biyu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

4581total visits,2visits today


Karanta:  Ambaliyar Ruwa Mafi Muni a Afirka a Shekara 20

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.