Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

Katafaren shafin sada zumunta na Facebook ya sake yin wata hobbasa, inda ya bullo da fasahar bidiyo, da za ta yi gogayya da YouTube da kuma tasoshin Talbijin.

Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

Nan gaba kadan masu amfani da Facebook za su ga sabon madannin Kallo, wanda zai ba su damar ganin shirye-shirye iri daban-daban, wasu daga ciki kamfanin ne ke daukar nauyinsu. Madannin mai suna ‘Watch’ zai dace da bukatun mutum, ta yadda mai amfani da Facebook zai iya gano sabbin shirye-shirye, bisa la’akari kan abin da […]

Barayi sun sace tirela makare da wayar iPhone 7

A kasar Neitherlands aka cafke mutanen biyar da suka fito daga kasar Romania, wadanda ake zargi da sace wayoyin iPhone 7, da suka kai $590,000, a lokacin da babbar motar daukar kayan ke tafiya a babbar hanya.

Barayi sun sace tirela makare da wayar iPhone 7

An yi zargin sun yi ta bin motar sau da kafa, daga bisani daya daga cikinsu ya yi tsalle ya dane motar, ya fasa wani gilashi ya shiga cikin ta. Daga nan sai ya fara miko manyan kwalayen da wayoyin ke ciki ta saman motar, sauran abokan satar shi na karba suna zubawa a cikin […]

Kamfanin Alhazai Express ya kaddamar da Manhajar Radio

Kamfanin Alhazai Express ya kaddamar da Manhajar Radio

Shahararren kamfanin fasaha dake jihar Kano a Nigeria, Alhazai Express, ya kaddamar da sabuwar manhajar Radio (Alhazai Radio) mai dauke da tashohin Hausa dama sauran yaruka kai tsaye a wayar tafi da gidan ka mai kirar Android. Kamfanin ya sanar da hakan ne a shafin sa ta sada zumunta dake Twitter dama Facebook baki daya. […]

An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

An kai karar kamfanin Kim Kardashian West saboda satar fasahar jakar selfie.

An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

Jakar saka wayar komai-da-ruwanka ta LuMee, wacce kamfanin Kimisaprincess Inc ke tallatawa, tana da wata fitila da ke taimakawa masu amfani da ita wurin daukar hoton dauki-da-kanka, selfie, mai kyau. Amma wani mutum mai suna Hooshmand Harooni ya bukaci ta biya shi $100m (£75m) saboda satar fasaharsa. Ya ce shi ne ya “kirkiro fitila da […]

Kaspersky na Rasha ya musanta aiki da hukumar leken asiri

Wani kamfanin tsaro mai mazauni a birnin Moscow ya musanta zargin ya yi aiki tare da hukumar leken asirin kasar, bayan zargin aikata hakan da kafafen yada labaran Amurka da gwamnati suka yi.

Kaspersky na Rasha ya musanta aiki da hukumar leken asiri

Shafin internet na Bloomberg ya rawaito cewa ya ga sakwannin email da ke nuna kamfanun Kaspersky ya samarwa hukumar leken asirin kasar bayanan. Kuma a ranar talata ne gwamnatin Amurka ta cire sunan kamfanin daga jerin sunayen wadanda aka amince ayi mu’amala da su. Sai dai kamfanin shugaban kamfanin Kaspersky Eugene Kaspersky ya dage cewa […]

Facebook da Whatsapp na bata tarbiyyar ‘yan mata — Sultan

Shugaban majalisar koli ta lamurran addinin Islama a Najeriya, ya gargadi yara musamman 'yan mata da su guji daukar lokaci mai yawa kan shafukan sada zumunta na zamani domin yin hakan ka iya bata tarbiyarsu.

Facebook da Whatsapp na bata tarbiyyar ‘yan mata — Sultan

Da yake jawabi a wajen wata gasar musabakar Alkur’ani mai girma a birnin Sakkwato ranar Lahadi, Sultan Saad Abubakar, ya ce, “abin damuwa ne matuka” ganin irin yadda shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Whatsapp da Instagram da 2go ke dauke wa yara hankali daga karatunsu. Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi […]

‘Snapchat na sanya rayuwar yara cikin hadari’

‘Snapchat na sanya rayuwar yara cikin hadari’

Makarantu na gargadin iyayen yara cewa sabon shafin sadarwa na Snapchat wanda ke nuna hakikanin wurin da mutum yake ka iya sanya rayuwar yara cikin hadari. Snapchat dai na bayar da dama ga masu amfani da shi da su bayyana hakikanin wurin da suke ga masu bibiyarsu. A wata wasika da BBC ta gani, wata […]

Na’urar ATM ta cika shekara 50 a duniya

Na’urar ATM ta cika shekara 50 a duniya

Shekaru 50 ke nan da fara amfani da na’urar fitar da kudi daga banki wato ATM Machine a duniya. A ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 1967 ne wani wani banki a birnin Landan ne ya fara amfani da na’urar. An samar da na’urar ne domin saukakawa mutane al’muransu musamman ta fuskar cire kudi […]

Jirgi mai samar da intanet ya yi tashi na biyu

Jirgi mai samar da intanet ya yi tashi na biyu

Facebook ya kammala gwada wani jirgin da ya ƙera maras matuƙi da ke amfani da hasken rana a karo na biyu, don samar da intanet ga yankuna masu rata na duniya. Jirgin – wanda aka yi wa laƙabin Aquila – ya tashi tsawon sa’a ɗaya da minti 46 a cikin yankin Arizona na Amurka. A […]