Magani Mai Fasahar Dijital Zai Shigo Kasuwa

Hukumomin Amurka sun amince a fara sayar da wata kwayar magani ta fasahar dijital karon farko a duniya.

Magani Mai Fasahar Dijital Zai Shigo Kasuwa

Kamfanin Japan mai suna Otsuka ne ya samu izinin sayar da nau’in maganin da yake sarrafawa don masu larurar kwakwalwa da ake kira Abilify dauke da wani dan kankanin maballi a kowacce kwaya. Da zarar an hadiyi kwayar maganin, sai ta aika sako zuwa wani abu da za a manna wa jikin maras lafiya wanda […]

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aiki.

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Najeriya ta san ‘yan hamayyar da ke daukar nauyin ‘yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu. Mista Jonathan ya ce bai […]

An Kaddamar da Shafin Softuwayar Hausa Irinsa Na Farko a Kano

A Kano cikin tarayyar Najeriya masana harshen Hausa da al'adun Hausawa da dalibai daga kasashen Nijar, Togo,Senegal da Mali suka hallara inda suka kaddamar da shafin softuwayar Hausa domin yin anfani dashi a kafar sadarwa ta zamani

An Kaddamar da Shafin Softuwayar Hausa Irinsa Na Farko a Kano

A karshen mako ne aka kaddamar da shafin softuwaya na Hausa irin sa na farko a Kano da nufin rayawa da bunkasa harshe da kuma al’adun Hausawa a duniya ta hanyar amfani da kafofifn sadarwar zamani na intanet. Manazarta da bincike kan harshen Hausa daga Jami’o’i da sarakunan gargajiya da dalibai kan ilimin harshen Hausa […]

Yadda Tsananin Kadaici Ke Juya Kwakwalwa

Kwakwalwar Sarad Shourd ta fara juyewa bayan an tsareta a kurkuku tsawon wata biyu. Ta rika jin takun sawun fatalwa da walkiya na haskawa, inda a mafi yawan kwanaki take shafe yini a sunkuye tana saurare ta kafar kofa.

Yadda Tsananin Kadaici Ke Juya Kwakwalwa

A wannan yanayin zafin, wannan mata ‘yar shekara 32 ta yi hawan tsauni tare da kawayenta a tsaunukan Kurdistan da ke kasar Iraki, a daidai lokacin da sojojin Iran suka kama su, bayan da suka kauce suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Iran. An zarge su da leken asiri, inda aka tsare su a wani […]

Kasashen Asiya zasu rage yawan robobi a teku

Kasashen Asiya zasu rage yawan robobi a teku

Kasashen da suka fi kowa alhakin gurbata tekunan duniya da robobi sun yi alkawarin tsaftace halayensu. A wajen wani taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, wakilai daga kasashen Sin, da Thailand, da Indonesiya da Philippines sun dau aniyar kawar da robobi daga tekuna. Amma basu rattaba hannu akan wata yarjejeniya ba, abin da masana […]

An yi garkuwa da tsohuwar ministar muhalli

An yi garkuwa da tsohuwar ministar muhalli

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeria ta ce an sace wata tsohuwar minista da mijinta. ‘Yan sandan sun ce an sace tsohuwar ministar ta Muhalli Laurencia Laraba Malam, da mijinta Mr Pious Malam a kan hanyar Abuja babban birnin kasar zuwa Kaduna. Kakakin rundunar ‘yan sandan ASP Aliyu Usman ya ce […]