Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce musulmai 'yan Rohingya a Myanmar na fuskantar wani nau'in wariya mai kama da ta launin fata karkashin jagorancin gwamnati.

Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Rahoton baya-bayan nan na Amnesty ya bayyana kauyukan Rohingya a matsayin kurkukun talala, inda ya al’ummomin suka shafe gomman shekaru suna fuskantar musgunawa. Mai aikowa BBC rahoto daga Kudu maso Gabashin Asiya na cewa rahoton Kungiyar Amnesty daya ne daga cikin takardun da kungiyoyin kare hakkin dan’adam ke tattarawa da yiwuwar shigar da manyan hafsoshin […]

Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci, abin da ya maido da kasar cikin jerin sunayen makiyan Amurka.

Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

A lokacin da ya ke ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasa mai tallafa wa ta’addanci a fadar White House, Trump ya ce, tun da jimawa ya kamata su dauki wannan mataki. Korea Ta Arewa na ci gaba da kasancewa cikin jerin takunkuman da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka kakaba ma ta saboda gwaje-gwajenta […]

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Tsoffin kawayen shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun yi kakkausar suka ga matakin da ya dauka na yin biris da kiraye-kirayen da ake masa a kan ya yi murabus.

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Shugaban kungiyar ‘yan mazan jiya, Chris Mutsvangwa, ya shaida wa BBC cewa, an riga an gama da Mr Mugabe a fagen siyasa domin babu wani tasiri da zai yi. Mai magana da yawun jam’iyyar kasar mai mulki ta Zanu-PF ya ce, yanzu Mr Mugabe ba shi da wani iko. Jam’iyyar wadda tuni ta cire shi […]

Donald Trump ya Sassauta Ra’ayinsa Kan Koriya Ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Koriya Ta Arewa da ta yarda a hau teburin tattaunawa don hakura da batun shirin makami mai linzaminta.

Donald Trump ya Sassauta Ra’ayinsa Kan Koriya Ta Arewa

Mista Trump ya furta hakan ne a wani taron manema labarai inda shi da shugaban Koriya Ta Kudu ke halarta, yayin wata ziyara da yake yi a Koriya Ta Kudun, mai cike da damuwa kan barazanar nukiliyar Koriya ta Arewa. Sai dai a wannan karon ya sauya irin kalamai masu zafi da ya saba furtawa […]

Kasar Jamus Ta Tallafawa Kananan Hukumomi Hudu a Jamhuriyar Nijar

Kasar Jamus da wasu kasashen nahiyar turai sun tallafawa kananan hukumomi hudu a Jamhuriyar Nijar da zummar dakile kwararar matasa zuwa kasashen turai

Kasar Jamus Ta Tallafawa Kananan Hukumomi Hudu a Jamhuriyar Nijar

Kananan hukumomi hudu na Junhuriyar Nijar ne kasar Jamus, a karkashin ma’aikatar harkokin wajen kasar, da wasu kasashen turai, suka tallafawa da zummar hana matasa yukurin ratsawa ta kasar Libya zuwa kasashen turai. Mukhtari Usman, shugaban hukumar mashawarta ta jihar Damagaran, ya yi godiya tare da fatar tallafin zai taimaka wajen kawo ci gaban yankunan […]

‘Yan majalisa sun mayar da cin hancin $8,000

‘Yan majalisa sun mayar da cin hancin $8,000

‘Yan majalisar kasar Uganda sun mayar da dala 8,000 kimanin fam 6,000 da aka ba kowannensu domin tsawaita mulkin shugaba Yoweri Museveni. Shugaba Museveni ya shafe shekara 31 yana mulkin Uganda. ‘Yan majalisun su takwas sun mayar da fam 8,000 da kak bai wa kowannensu domin su tuntubi al’umominsu game da wani kuduri mai cike […]

Za a kona gawar Sarkin Thailand shekara guda bayan rasuwarsa

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Bangkok don martaba gawar Sarkin Bhumibol Adulyade.

Za a kona gawar Sarkin Thailand shekara guda bayan rasuwarsa

Sarkin ya mutu ne a watan Oktobar shekarar 2016, yana da shekara 88. An fara bukuwan binne marigayin ne a ranar Laraba kamar yadda tanadin addinin Buddha ya shinfida. Galibin gidajen da ke birnin an lullube su da kyallaye masu ruwan dorawa, yayin da jama’a suka sanya bakaken tufafi. A ranar Alhamis ne za a […]

Burundi ta Fice Daga Kotun ICC

Burundi ta kasance kasar ta farko a nahiyar Afirka da ta fice daga Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Burundi ta Fice Daga Kotun ICC

Tun a bara ne dai kasar ta sanar da Majalisar dinkin duniya cewa za ta fice daga kotun. Ha kuma wannan lamari ya tabbata a yanzu. A yanzu dai ana yi wa wannan batu kallon zakaran gwajin dafi ga yunkurin samar da adalci ko shari’a a tsakanin kasa da kasa. Batun dai ya ba mutane […]

Tillerson ya kai ziyarar tankwabe fada-a-jin Iran

Tillerson ya kai ziyarar tankwabe fada-a-jin Iran

Sakataren wajen Amurka Rex Tillerson ya isa birnin Riyadh don fara ziyarar kwana shida a Saudiyya da kuma makwabciyarta Qatar. Tillerson zai sake matsa lamba don kawo karshen kaurace wa Qatar da Saudiyya tare da wasu kawayenta suka yi saboda zargin mara baya ga musulmi masu tsattsauran ra’ayi. Sai dai ana sa rai ziyarar ta […]

An yi tir da ba Robert Mugabe mukamin farin jakada

An yi tir da ba Robert Mugabe mukamin farin jakada

Kungiyoyin kare hakkin dan’adam da jam’iyyar adawa a Zimbabwe sun yi tir da shawarar Hukumar Lafiya a Duniya ta nada Shugaba Robert Mugabe matsayin farin jakada Kungiyar Human Rights Watch ta ce la’akari da tarihin Mugabe kan batun ‘yancin bil’adama, abin kunya ne ba shi irin wannan mukami. Jam’iyyar adawa a Zimbabwe ta ce matakin […]

1 2 3 23