Gobara ta tashi a kurkukun Kuje na Abuja

Gobara ta tashi a kurkukun Kuje na Abuja

Wata gagarumar gobara wadda ta lashe gine-gine da yawa ta tashi a cikin kurkukun Kuje, dake Abuja. Gobarar wadda ta fara da misalin karfe 10:45 na safe, ta yi barna matuka. Wata kungiya wadda ta kira kanta da ‘Mai Yaki da rashin adalci kan fursunoni ta Najeriya (PAIN), ta dauki alhakin tashin gobarar. PAIN ta […]

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

Hukumar Yakin da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) tare da sauran hukumomi sun sami nasarar kwace wasu haramtattun kwayoyi da yawansu ya kai kilogaram 881.100, sakamakon wani sumamen hadin gwiwa na musamman da aka gudanar a Jihar Sokoto da kuma wasu yankuna tsakanin bodar Najeriya da Nijar. Shugaban hukumar, Kanar Muhammad Mustapha Abdallah (Mai […]

An sake kai hari Jami’ar Maiduguri

An sake kai hari Jami’ar Maiduguri

Rahotanni dake fitowa daga birnin Maiduguri na Jihar Borno, na cewa ‘yan kunar bakin wake sun sake afkawa cikin Jami’ar Maiduguri, inda biyu daga cikinsu suka tashi wani abu mai fashewa dake jikinsu. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na daren Alhamis, a inda wasu da suka shaida lamarin sun ce wasu mutane […]

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

  Tun a ‘yan watannin baya ne dai takaddama ta barke tsakanin  Magajin garin na Sokoto da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, bisa nadin sarautar Marafan Sokoto, da mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi wa Alhaji Inuwa Abdulkadir, tsohon Ministan Wasanni da Matasa. Kan wannan al’amari ne tsohon Magajin gari mai […]

Dan Masanin Kano Maitama Sule ya rasu

Allah ya yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a ranar Litinin da safe bayan ya sha fama da jinya.

Dan Masanin Kano Maitama Sule ya rasu

Wata majiya daga iyalansa ta tabbatarwa da BBC rasuwar, amma babu wani karin bayani zuwa lokacin wallafa wannan labari. Ya rasu ne a kasar Masar inda ya yi jinyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan kasar […]