Giwaye da damusa sun hana mutane sakat a kauyukan Indiya

Giwaye da damusa sun hana mutane sakat a kauyukan Indiya

‘Yan kabilar Paharia da ke zaune a tsaunukan da ke yankin Jharkhand a kasar Indiya, sun kwashe kwanaki ba tare da sun runtsa ba. Wata giwa ta tumurmushe a kalla mutum 15 har lahira a ‘yan watannin da suka gabata. Daga can arewacin yankin kuma, wasu kauyaywa da ke zaune kusa da wani gandu ajiye […]

Wata tsohuwa ta kammala digiri a shekara 91

Wata tsohuwa 'yar kasar Thailand mai shekara 91 ta ce, "Gemu ba ya hana neman ilimi", inda ta kammala digirinta bayan ta shafe shekara goma tana yi, a tattaunawar da suka yi da wakilin BBC.

Wata tsohuwa ta kammala digiri a shekara 91

Kimlan Jinakul, tana da burin ta yi karatu a jami’a, sai dai ba ta samu wannan damar ba a lokacin da take da kuruciya. Daga baya ne lokacin da ta ga yawancin ‘ya’yanta sun kammala karatu a jami’ar, sai ta yanke shawarar fara karatun nata, kuma a ranar Larabar nan ne ta kammala digiri. Kimlan […]

An kama wani mawaki kan yin rawar dab a Saudiyya

An kama wani sanannen mawaki a Saudiyya saboda yin rawar dab yayin wani taron rawa da waka a a kudu maso yammacin kasar.

Abdallah Al Shahani, wani mai gabatar da shiri a talbijin, jarumin fina-finai, kuma dan asalin kasar Saudiyya, ya yi rawar ne wacce ake rufe goshi a dan rankwafa a yayin wani taron wakoki da aka yi a birnin Taif cikin karshen makon da ya gabata. An haramta rawar dab a kasar, saboda hukumomi na ganin […]

An Kaddamar da Burodin Kwankwasiyya

An Kaddamar da Burodin Kwankwasiyya

Wani kamfanin yin burodi a Najeriya ya kaddamar da wani sabon nau’in burodi a cikin jerin wadanda ya saba yi. Shi dai wannan burodi mai suna Kwankwasiyya ya samu tagomashi daga bangorin al’umma daban-daban wanda ya hada da jarumai na masa’antar shirya fina finan Hausa mai suna Kannywood a matsayin jakadun burodin Kwankwasiyya.   The ambassador’s […]

Ka san illolin kaifin basira kuwa?

Kana jin basira za ta iya kasancewa matsala mai ban takaici maimakon alheri mai tarin amfani? Watakila ka amince da haka ko kuma ka kekasa kasa ka ce ba ka yarda da wannan magana ba, ko?

Ka san illolin kaifin basira kuwa?

Yi nazarin wannan binciken da David Robson ya yi wa BBC Idan jahilci alheri ne, ko basira za ta iya zama masifa? Yawancin mutane za su ce haka abin yake. Muna daukar mutanen da suke da baiwa a matsayin wadanda suke tattare da wata damuwa da kadaici. Ka duba mutane irin su Virginia Woolf da […]

‘Yan Matan Najeriya Da Ake Safararsu Italiya Na Fadawa Harkar Karuwanci

Yawan yara mata 'yan Najeriya da ake safararsu zuwa kasar Italiya domin yin karuwanci na kara karuwa.

‘Yan Matan Najeriya Da Ake Safararsu Italiya Na Fadawa Harkar Karuwanci

Ma’aikatan wayar da kan jama’a na kasar Italiya sunce akwai babban sauyi ga yadda bakin hauren Afirka ke shiga kasar, inda ake ganin cewa mafi yawan ‘yan mata daga cikinsu duk daga Nijeriya suke fitowa, kuma suna zuwa ne da sanin cewa karshenta zasu karkare ne a matsayin karuwai. Amma yawancin ‘yan matan basu da […]

‘Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa’

‘Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa’

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya ce Najeriya na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa. Shugaban Asusun a Najeriya, Anthony Lake, ne ya bayyyana haka a wurin taro kan ‘makon shayar da nonon uwa’ a Abuja, babban birnin kasar. A cewarsa, kudin da mata ke kashewa […]

Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

‘Yan sanda na zargin wani mutum da kashe matarsa a cikin jirgin ruwa a jihar Alaska ta Amurka saboda “ta ki daina yi masa dariya”. Ana zargin Kenneth Manzanares da laifin kisan matarsa mai shekara 39, wacce aka gano gawarta an yi mata raunuka da dama a kanta a cikin jirgin ruwan. An tsare shi […]

Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’

Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’

Hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya yi kasa a jerin masu kudin duniya inda ya fado daga mataki na 51 zuwa 105, in ji mujallar Forbes. Mujallar ta ce arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a shekarar 2016 zuwa biliyan 12.2 a bana. Hakan dai ya faru ne, a cewar […]

‘Nigeria za ta sha gaban Amurka wajen yawan al’umma’

‘Nigeria za ta sha gaban Amurka wajen yawan al’umma’

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya a kan yawan al’ummar Duniya na shekarar 2017 ya ce Najeriya za ta sha gaban Amurka a yawan al’umma.. Haka zalika rahoton ya yi hasashen cewa kasar za ta kasance ta uku mafi yawan al’umma a duk fadin duniya nan da shekarar 2050. Rahoton wanda aka fitar a ranar […]