Tattaunawa Tsakanin Mukadashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Da Kwamuti Ta IPI

Dazu anyi tattauna da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kwamuti ta IPI wanda mukaddashin shugaban kasa yace mulki General Muhammadu Buhari zai hada kai da kwamuti din IPIN

Tattaunawa Tsakanin Mukadashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Da Kwamuti Ta IPI

Dazu  anyi tattauna da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kwamuti ta IPI wanda mukaddashin shugaban kasa  yace mulki General Muhammadu  Buhari zai  hada kai da kwamuti din akan kungiyar yada labarai ta duniya. Ya bada tabbacin ne a lokacin da kwamuti ta ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja akan shirya tsarin  […]

Iyaye a Kano sun koka game da yawaitar satar yaran su kanana

Iyaye a Kano sun koka game da yawaitar ayyukan bata gari na satar yaran su kanana a wasu sassan birnin, lamarin da sukace na barazana ga makomar iyalai da al'uma baki daya.

Iyaye a Kano sun koka game da yawaitar satar yaran su kanana

Daga watan Janairun bana zuwa yanzu kididdiga ta nuna cewa an sace yara kanana yan kasa da shekaru 5 kimamin tamanin daga wasu unguwanin birnin Kanon Dabo. Wasu iyaye sun yiwa wakilan sashen Hausa na VOA Mahmud Ibrahim Kwari bayanin yadda aka aka sace ‘ya’yansu. Wata mace ta baiyana yadda kimamin watani goma sha daya […]

Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya – UNICEF

An gudanar da taro tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin yara daga kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki akan batun cin zarafin yara da a halin yanzu ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriyar.

Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya – UNICEF

Wani bincike da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi, ya gano cewa ana cin zarafin kananan yara shida cikin 10 a Najeriya. Binciken har ila yau ya nuna cewa ana kuma muzgunawa kashi 50 cikin 100 na kananan yara a kasar. Hakan ya sa masu ruwa da tsaki suka ga […]

Zaben Anambra: ‘Yaran Nnamdi Kanu za su gane kurensu’

Zaben Anambra: ‘Yaran Nnamdi Kanu za su gane kurensu’

Rundunar ‘yansandan Nigeria ta ce ta daura damarar yin maganin duk wani gungun mutane da za su nemi kawo rudani ko hana gudanar zaben gwamnan da za a yi a jihar Anambra ta shiyyar kudu-maso-gabashin kasar. ‘Yansandan na mayar da martani ne ga barazanar da kungiyar ‘yan aware ta IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ke […]

Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33

Bayanai daga jihar Kano na cewa kungiyar kwadagon jihar ta ce mambobinta na bin hukumomi makudan kudaden fansho da sauran hakkokin ma'aikata.

Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33

Kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya reshen jihar kano, ta ce ta na bin gwamnatin jihar kano bashin sama da Naira bilyan 33, a zaman kudin fansho da hakkin ma’aikata. Saboda haka ne kungiyar kwadagon take tuni ga gwamnatin jihar da ta saka batun ma’aikata a sahun farko idan ta fara kasafta kudaden da ta […]

An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

A Najeriya, hukumomi sun kori wata kara da aka shigar ana tuhumar wani mutum mai shekara 41, wanda ya sanya wa karen sa sunan Shugaba Muhammadu Buhari. An kama Joachim Iroko, wani dan kasuwa da ake cewa Joe Fortemose Chinakwe, a shekarar 2016, bisa zargin sa da neman tayar da rikici a kasar. Wani alkali […]

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun koka a kan hali da mutanen Mambila ke ciki

Hadakar kungiyoyin kare hakkin bil Adama ta koka game da halin ko in kula da shugabanin ke nunawa akan halin da yan gudun hijira na yankin Mambila a jihar Taraba suke ciki, musamman ta fuskar kiwon lafiya.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun koka a kan hali da mutanen Mambila ke ciki

Kungiyoyin sun ce yan gudun hijiran musamman wadanda suka ketara zuwa kasar Kamaru na bukatar agaji, musamman daga gwamnatin jihar. Hadakar kungiyoyin kare hakkin bani adaman da kuma yan fafutuka da suka hada da Centre For Human and People’s Right Advocacy da Taraba Concern Citizens Forum, sun koka ne a lokacin da suka kai ziyarar […]

1 2 3 4