Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Kamaru ta yi kunnen doki 1-1 da Australia a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Zakarun na Afirka su ne suka fara jefa kwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, ta hannun Zambo Anguissa. Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne kuma […]

Salah ya koma Liverpool a kan fam miliyan 34

Salah ya koma Liverpool a kan fam miliyan 34

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta kammala cinikin dan wasan Roma Mohamed Salah a kan fam miliyan 34. Dan kasar Masar, Salah mai shekara 25 da haihuwa, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ne da Liverpool. A shekarar 2014 dan wasan ya so ya koma Liverpool, amma sai ya koma kulob din Chelsea. Kocin Liverpool, Jurgen […]

Messi zai biya tara maimakon zaman gidan yari

Messi zai biya tara maimakon zaman gidan yari

Akwai yiwuwar shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi zai kaucewa daurin wata 21 a gidan yari inda ya zabi ya biya tara, kamar yadda rahotanni daga kasar Spain suka bayyana. Wata kotu ce a Spain ta samu dan wasan da laifin zambar haraji. Babban mai gabatar da karar kasar zai musanyawa Messi zaman gidan yari […]

Aston Villa tana zawarcin John Terry

Aston Villa tana zawarcin John Terry

Kungiyar Kwallon Kafa ta Aston Villa tana zawarcin tsohon kaftin din Ingila John Terry. Kodayake an yi nisa a batun cinikin dan wasan bayan, ana saran kammala cinikinsa ne zuwa mako mai zuwa. Terry, mai shekara 36, zamansa zai kare a Chelsea ne a ranar 30 ga watan Yuni. Kungiyoyi da dama ne suka bayyana […]

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Jamus da chile su ka tashi kunnen doki 1-1 a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez shi ne ya ci wa Chile kwallonta minti shida da fara wasa bayan da Arturo Vidal na Bayern Munich, ya zura masa kwallon da dan […]

Crystal Palace na shirin nada De Boer kociya

Crystal Palace na shirin nada De Boer kociya

Crystal Palace ta ba wa tsohon dan wasan Holland Frank de Boer mai shekara 47, kociyanta kuma tattaunawa ta yi nisa kan kwantiragin da za su kulla. De Boer zai gaji Sam Allardyce, wanda ya bar kungiyar bayan ya ceto ta daga faduwa a gasar Premier a kakar da ta kare. De Boer wanda ya […]

Di Maria ya yarda da laifin kin biyan haraji

Di Maria ya yarda da laifin kin biyan haraji

Tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria ya amince ya biya tarar Euro miliyan biyu a kan tuhumarsa ta zambar kudin haraji. Hukumomin Spaniya sun ce dan wasan zai amince da laifi biyu da ake tuhumarsa da su a lokacin yana Real Madrid, laifukan da suka danganci harkokin kudinsa, wanda a kan hakan ne […]

Yadda ‘yan kwallo Musulmai ke jure taka leda a lokacin azumi

Yadda ‘yan kwallo Musulmai ke jure taka leda a lokacin azumi

An buga wasannin kasa da kasa na wannan makon jiya ne cikin watan Ramadan, lokacin da Musulmai a fadin duniya ke azumin wata daya. Dole kociyoyin kasasen da mafi yawansu Musulmai ne su nemi dabarun taimaka wa tawagar ‘yan wasansu, wadanda yawancinsu ke azumi daga sanyin safiya zuwa maraice. Watan Ramadan ya zo daidai da […]