Shekaru Biyu Da Mulkin APC: Gwamnati Ba Ta Yi Aikin Komai Ba — Hassan Hyat

Hassan Hyat

‘Yan siyasa da masu tsokaci kan al’umuran yau da kullun na ci gaba da yin tsokaci kan yadda zababbun da aka zaba a shekara ta 2015 suka ja silin zaren mulki ko wakilcin da aka aka zabe su a kai. Wakilinmu ISA BALARABE ya sami damar jin ta bakin wasu manyan ‘yan siyasar jihar Kaduna, inda ya samu zantawa da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, kuma Tsohon Ministan Sufuri, MISTA FELID HASSAN HYAT, wanda kuma ya bayyana cewa shi dai a wajensa, jam’iyyar APC ba ta tsinana wa al’ummar kasar nan komai ba a wadannan shekaru biyu da ta yi tana mulki. Ga yadda hirarsu ta kasance.

Kwanan nan ne jami’yya mai mulki ta APC ta cika shekara biyu a kan karagar mulki. A matsayinka na dan hamayya, ya ka ga wadannan shekaru?

Ai shekara biyun nan, ba abin da zan ce an samu, sai ma koma-baya da aka samu a Nijeriya ta bangarori da dama.

Me kake nufi da koma-baya?

Kafin zaben 2015 kowa ya san jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin abubuwa uku, wato tsaro da kawo karshen cin hanci da kuma bunkasa tattalin arziki, to me aka yi? Kuma sun ce in sun ci zabe za a rage farashin man fetur,duk dan Nijeriya ya san kari aka yi a farashin man fetur fiye da yadda mafiya yawan ‘yan Nijeriya ke tunai. To wannan ci gaba ne aka samu ko kuma koma-baya?

Batun tattalin arzikin kasar nan kuma, an ce in APC  ta ci zabe za a lura da mutuncin Naira a kasuwar canji a sassan duniya, to yanzu matsayin Naira na gaban Dala ne ko kuwa Dala ce ke gaban Naira a kasuwannin duniya?

Karanta:  Jam'iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Amma jam’iyyar APC su cewa suke sun sami nasara a batun tattalin arzikin. To kai ka yarda nasarar da ake cewar an samu?

Ga wadanda suka san yadda tattalin arzikin Nijeriya ke ciki a lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki ya san matsayin Naira ya kuma san matsayin Dala. Yanzu za mu ce an cika mana alkawari ne ko kuma akasin cika alkawarin aka samu?

Wasu na cewa an sami ci gaba a bangaren zaman lafiya, to babu zaman lafiyar da ya dace sai adalci a mulkin da ake yi. Yanzu aikin gwamnati a shugabancin APC daga ‘yan uwa sai ‘yan ‘yan jam’iyyarsu ta APC. To wannan adalci ne? Sai kuma nadin mukami a bangare guda, wannan ba adalci ba ne.

To ya ka dubi batun yakar cin hanci da gwamnati ta sa a gaba a shekara biyu da suka gabata?

Lallai ko ana yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nijeriya, amma fa ka sani yakin ya tsaya ne ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP, mu ake kamawa, mu kuma ake tsarewa. Amma an kama ‘ya’yan jam’iyyar APC tun da su ‘ya’yan mowa ne, ba a fito an ce an kai su kotu ba, sai dai a ce an kafa kwamitin bincike, daga nan sai ka ji shiru, tamkar an aiki bawa garinsu.

To, wannan shi ne yaki da cin hancin da aka yi mana alkawari kafin zabe?

To wane tunani ka ke yi ga halin da ‘yan Nijeriya ke ciki a yau da gwamnati mai ci ta cika shekara biyu?

Ai tunanina a bayyane suke, ’yan Nijeriya sun zabi gwamnati mai kin cika masu alkawari, sun zabi masu korarsu aiki, sun zabi masu rushe masu gidajensu da kasuwanni. Ai yanzu ‘yan Nijeriya Jam’iyyar PDP za su sake zaba a 2019 in Allah ya kai mu.

Asalin Labari:

LEADERSHIP Hausa

567total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.