Shugaban Majalisar Dokokin Kano ya yi murabus

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a Najeriya Kabiru Alhassan Rurum ya yi murabus, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban ya yi murabus ne tare da mataimakin shugaban masu rinjaye Mai-fada Bello Kibiya.

Ana zargin Alhassan Rurum da aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci. Sai dai shugaban ya musanta aikata wani laifi.

Har ila yau, ya ce ya yi murabus ne saboda ya bayar da damar gudanar da bincike a kansa.

Daga nan ne sai ‘yan majalisar suka zabi Abdullahi Yusuf Atta wanda yake wakiltar mazabar karamar hukumar Fage a matsayin sabon shugaba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

178total visits,2visits today


Karanta:  Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

Leave a Reply

Your email address will not be published.