Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota yayin da yake barin filin jirgin saman birnin Harare bayan ya dawo daga tafiya.

Ko da yake, shugaban bai ji rauni ba, amma mai dakinsa Grace wadda suke tare a mota ta jikkata.

Shugaban ya sauka a filin jirgin saman ne yayin da ya dawo jinya daga kasar Singapore.

Misis Grace ta kuje ne a idon sawunta na dama kuma an garzaya da ita wani asibiti da ke kusa kafin daga bisani a sallame ta.

Fadar shugaban kasar ba ta bayyana abin da ya jawo hatsarin ba.

Wani ganau ya ce ya ga gawar daya daga cikin direban baburan da ke yi wa shugaban kasar rakiya a wurin da al’amarin ya faru.

Ana yawan samun hadurra a titunan kasar Zimbabwe kuma galibi yana faru ne dalilan yadda ayarin motoci suke yawan guje-guje.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1550total visits,1visits today


Karanta:  An amince matan Tunisia su auri mazan da ba Musulmi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.