Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya ne a kowacce rana ke ci gaba da ficewa daga Myanmar zuwa makwabtaka don tsira da rayukansu bayan kisan kiyashin da ake ci gaba da yi musu a yankin Rakhine.

Karon farko tun bayan barkewar rikicin baya-bayan nan a Myanmar da ya hallaka Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da dama baya ga tilastawa daruruwa barin gidajensu, shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta ce gwamnatin na kokarin kare hakkin kowanne bangare a Rakhine.

Kalaman Aung San Suu Kyi na zuwa ne bayan kiran da MDD ta yi wa gwamnatinta na kawo karshen rikicin da ya tilastawa musulmi ‘yan kabilar Rohingya kimanin dubu 146 barin gidajensu zuwa Bangaladesh.

Shugabar gwamnatin ta yi ikirarin cewa dukkanin kalaman da ke zaga kafafen yada labarai tsagwaron karya ce da bata da tushe, tana mai cewa hakan baya rasa nasaba da muradan ‘yan ta’adda.

Ms Suu Kyi wadda ke sanar da hakan yayin tattaunawa da shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya ta wayar tarho, wanda ya nuna damuwa kan wariyar da ake nunawa al’ummar Musulmi a kasar, ta ce gwamnatinta na daukar matakan bayar da ‘yanci ga kowanne dan kasar.

MDD dai ta ce cikin makwanni biyu da fara rikicin wanda ya faro ranar 25 ga Oktoban da ya gabata kimanin ‘yan Kabilar Rohingya mutum dubu dari da arba’in da shida ne suka tsallaka iyaka zuwa makwabtan kasar lamarin daya kara adadin ‘yan kabilar da ke samun mafaka a kasashen ketare zuwa sama da dubu 400.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya dai ta ce a kowacce rana adadin ‘yan kabilar ta Rohingya da ke samun mafaka a kasashen ketare na kara yawaita cikin shekaru 40 da suka gabata.

Asalin Labari:

RFI Hausa

643total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.