‘Snapchat na sanya rayuwar yara cikin hadari’

Makarantu na gargadin iyayen yara cewa sabon shafin sadarwa na Snapchat wanda ke nuna hakikanin wurin da mutum yake ka iya sanya rayuwar yara cikin hadari.

Snapchat dai na bayar da dama ga masu amfani da shi da su bayyana hakikanin wurin da suke ga masu bibiyarsu.

A wata wasika da BBC ta gani, wata makaranta ta ce shafin na kawo “babbar matsala ga kariyar mutane” saboda za a iya bibiyar yaran ta hanyar amfani taswirar shafin.

Sai dai kamfanin na Snapchat, wanda ke tafiyar da shafin, ya ce kunna manhajar ake yi, kuma za a iya rufe ta a ko wanne lokaci.

Mene ne taswirar Snapchart (Snap Map)?

An kaddamar da shafin Snap Map ranar 21 ga watan Yuni wanda zai bayar da dama ga mutane su binciko bangaren da suke da hotuna da bidiyoyin da aka wallafa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

413total visits,1visits today


Karanta:  Barayi sun sace tirela makare da wayar iPhone 7

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.