Sojoji sun ceto masu bincike da Boko Haram suka yi wa Kwanton Bauna

Wasu rahotanni da suke fitowa daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno na tabbatar da cewar Sojoji sun ceto gugun mutane nan masu binciken albarkatun kasa wadanda suka hada da ma’aikatan NNPC da kuma Jami’ar Maiduguri, wadanda ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa kwanton bauna a yau.

Majiyar dai ba ta bayyana a ina suke ba a halin yanzu saboda yanayi na tsaro, ta shaidawa Yerwa Express News cewar, tun farko dai wani jami’in tsaro na sa kai wato Civilian JTF, Ibrahim Abba Alhaji wanda ya samu nasarar tsarewa duk da harbin bindiga dake jikinsa, ya bayyanawa manema labarai yadda al’amarin ya faru.

“Akan hanyar mu ta shigowa Maiduguri, kushan kilomita 20, bayan kammala aikin da mu ka je yi na binciken albarkatun danyen mai, kawai sai muka ga baburan mashin na bullowa ta ko’ina daga Bornoyuse. Hakazalika, wadansu ababen hawa su ma suka dirar mana tare da bude wutar bindiga a kanmu ba kakkautawa”.

“jami’in ya kara da cewar, jerkin gwanon motoci 9 muke tafe da su, dukkansu kowacce na dauke mutane 10 a ciki. A yanzu motar mu ce kawai ta tsira, bayan mun share sama da kilomita 20 da fasassun tayoyi guda 2 da kuma harbin da aka yi wa mai jan motar ta mu”.

“Mun so mu far musu, amma jami’an sojoji da muke tare suka yi mana alamar mu kara gaba. Lamarin da ya janyo wadansu ‘yan Boko Haram suka biyo mu akan babura, anan ne muka fara musayar wuta a tsakanin mu”. Ibrahim ya kara da cewa “Hudu daga cikin mu wadanda suka samu raunuka, muna nan muna karbar taimako daga wajen likitoci, amma ban san halin da sauran ke ciki ba”.

Karanta:  Za a Rataye Sojan Nigeria Kan Kisan Abokiyar Aikinsa

 

 

 

Asalin Labari:

Yerwa Express News, Muryar Arewa

1832total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.