Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Rundunar Sojin Nigeriya ta fara janye jam’anta a hankali wadanda ta girke a wuraren duba ababan hawa a garin Aba bayan fadan da aka gwabza da masu zanga-zangar kafa Kasar Biyafara (IPOB)

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya wato NAN ya rawaito ranar Lahdi Gwamna Okezie Ikpeazu na fadawa manema labarai a Umuahia cewa an janye sojojin da ake musu take da Rawar Miciji II daga jihar.

Sai dai binciken da kamfanin dillancin labarai na NAN ya gudanar ranar Litinin yayi nuni da cewa ‘yan kalilan kawai daga cikin sababbin shingayen sojojin da aka kafa a tsakiyar birnin aka janye.

Shingaye biyar da aka kafa a kan titin nan mai yawan zirga-zirgar ababan hawa na Enugu zuwa Fatakol sun ragu zuwa guda uku.

Wani mai hayar babur mai kafa uku Emeka Chukwuma, mazaunin birnin ya fadawa NAN cewa shingayen sojin na kawu cunkoson ababan hawa sosai.

Yayi kira ga gwamnan jihar Ikpeazu ya shawo kan mahukunta soji don su janye shingayen ababan hawa don samun saukin zirga zirga.

Duk da haka, harkok na dawowa yadda suke a baya a garin na Aba bayan hatsaniyar da ta faru tsakanin sojojin da masu rajin kafa kasar Biyafara.

An bude kasuwanni bayan dokar takaita zirga-zirgar kwanaki biyar da gwamnan ya saka a garin

Yawancin shaguna a Babbar Kasuwar Ariaria, Sabuwar kasuwa, Kasuwar makabarta an sake bude su haka kuma ‘yan kasuwa sun cigaba da kasuwancinsu yadda suka saba

511total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.