Sojojin Najeriya Sun Ceto Wani Jirgi Daga Masu Fashin Teku

Dakarun sojojin ruwan Najeriya sun ceto wani katafaren jirgin daukar Mai daga hannun masu fashi akan Teku

Hedkwatar Sojojin ruwan Najeriya tace dakarunta sun ceto wani katafaren jirgin ruwa na kasashen Turai da ‘yan fashin teku su kayi yunkurin sace shi a yankin Niger Delta.

Darakatan labarai a hedkwatar Sojojin ruwan Najeriya Navy Captain Suleiman Dahun, yace su dai wadannan ‘yan fashin Teku sunyi kokarin garkuwa da babban jirgin ruwan Man na kasashen Turai amma Sojan ruwan Najeriya sun ceto shi.

Masanin harkokin Teku Abubakar Abdulsalam, yace irin wannan ko kadan baya bashi mamaki koda yake ya kara dacewa yakamata gwamnati da tabbatar da ganin cewa Sojoji na sintiri akan ruwan Najeriya a kowane lokaci domin karfafa tsaro akan Teku.

A cewar kwararru akan tattalin arziki a Najeriya, Yusheu Aliyu, yace irin wannan aika aika na kawo nakasu ga tattalin arzikin kasa, haka ma kamfanonin da suke daukar mai daga Najeriya suma suna tafka hasara da dama saboda idan aka kama jiragen su suna hasaran kudade masu yawa itama kasar tana hasara man da zata siyar domin idan aka sace man kasar ne ke da hasara.

Asalin Labari:

VOA Hausa

530total visits,2visits today


Karanta:  Za a halatta kananan matatun mai a Naija Delta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.