Sojojin Nijeriya Sun Kashe Mataimakan Shekau Biyu Ranar Sallah

Rundunar sojin Nijeria ranar Talata sun ce sun kashe wasu Kwamandojin Boko Haram biyu a wani hari da sukayi nasarar kaiwa  Alafa dake Borno ranar sallah.

Mai Magana da yawun Sojin, Brig-Gen Sani Usman a wata sanarwa da ya fitar yace Kwamandojin da aka kashe mataimakan shugaban Boko Haram ne tsagin Abubakar Shekau.

Kwamandojin Boko Haram din da aka kashe sun hada da Afdu Kawuri da Abubakar Banishek.

Ya kara da cewa, “Wannan ya hada kari kan Ba’Abba Ibrahim da wasu kwamandoji biyu da suka mutu bayan samun raunuka lokacin arangamar da akayi a Karamar Hukumar  Magumeri ta jihar Borno,”

Tuni aka gama da wasu jiga-jigan kungiyar guda biyar kuma na hannun daman Shekau a wani harin bom a watan Agusta

Usman ya bayyana faifen bidiyon da Shekau ya fitar kwanannan da cewa ba komai bane illa son cusa tsoro a zukatan ‘yan kasa masu son bin doka da oda.

A faifen bidiyon dai ‘yan kungiyar sun karyata kashe kwamandojinsu biyar sun kuma ce sunyi bukukuwan sallah lafiya a dajin na sambisa.

“Muna kalubalantar shugaban na ‘yan ta’addar da ya fito da mutanen da muka kashe ko kuma faifen bidiyon su idan har suna raye basu mutu ba.

“Har ila yau, ya kamata a fahimci cewa Shekau ya tsorata da kwanaki 40 din da Shugaban Sojin Kasar ya bawa LAFIYA DOLE da su kamo shi duk inda yake,” a cewar Usman din.

684total visits,5visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.