Sojojin Ruwan Najeriya Sun Isa Yankin Niger-Delta

Hedikwatar rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ta girke manya-manyan jiragen yakinta har guda shida a yankin Niger-Delta.

Yayin da wa’adin sintirin Operation Tsare Teku ke zuwa karshe, rundunar sojan ruwa ta ‘kara wa’adin ci gaba da gudanar da sintirin.

A cewar kakakin hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Captain Suleman Dahun, rundunar ta ‘dauki matakin ne domin kawo karshen ‘yan fashin teku, inda yace a shekarar da ta gabata sun kai hare-hare har 55 inda suka sami nasara har sau 36.

Masana harkokin tsaro a Najeriya, na ganin matakin yazo a dai-dai lokacin da ya dace.

Masanin tsaro Ahmed Tijjani Baba Gamawa, na ganin wannan na kama da wanda ‘yan magana kan kira na ‘ayita ta kare’ ganin yadda aka girke manya-manyan jiragen yaki har guda shida baya ga masu saukar ungulu daga sama.

Abin jira a gani shine irin yadda wannan karin lokaci zai shafi sha’anin tsaro a yankin Niger-Delta.

Asalin Labari:

VOA Hausa

836total visits,2visits today


Karanta:  Yan Sanda a Jihar Ogun Sun Kama Masu Satar Yara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.