Sojojin Syria Sun Sanar da Tsagaita Wuta a Gabashin Ghouta

Sojojin Syria sun sanar da tsagaita wuta a wata sanarwa da suka fitar a gabashin Ghouta dake wajen babban birnin kasar wato Damascus.

Hakan yazo bayan kasar Rasha wacce take abokiyar kawancen Syria ta bayyana cewar ta samu cimma matsaya da masu tsatsatsauran ra’ayi domin rage tashin hankula a shiyar. Sai dai masu hashashe suna tantamar aiwatar da hakan.

Gabashin na Ghouta yana daya daga cikin yankunan da aka so a tsagaita wuta a wata yarjejeniya tsakanin Rasha, Turkiyya da Iran a watan Mayu.

Sanarwar ta Sojojin Syria tace za’a fara debe wadanda suka jikata da misalin karfe tara na GMT a ranar Asabar.

Kungiyar ‘yan tawaye ta Faylaq al-Rahman ta murnar dakatar da tsagaita wutar, kuma tayi kira ga gwamnatin Syria da ta girmama hakan.

Asalin Labari:

BBC Hausa

811total visits,2visits today


Karanta:  Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.