An Shirya Taron Fadakar Da Manoma Da Makiyayan Nijar

Rikicin manoma da makiyaya babbar matsala ce da ke yawan addabar kasashen nahiyar Afirka, lamarin da kan janyo hasarar rayuka da dumbin dukiyoyi. Hakan ya sa wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar d ake kira FRAPS ta shirya wani taron wayar da bangarorin biyu kan muhimmancin zaman lafiya.

An Shirya Taron Fadakar Da Manoma Da Makiyayan Nijar

Wata kungiya mai zaman kanta da ke bin diddigin harkar manoma da makiyaya da ake kira FRAPS a takaice, ta shirya wani taron bita da ya tattaro manoma da makiyayan Jmahuriyar Nijar domin a tattaunawa. Kungiyar ta tattaro bangarorin biyu ne daga jihohin Maradi da Damagaram da Diffa domin kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu […]