Wani matashi ‘ya kashe mahaifinsa’ saboda aure a Jigawa

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa a arewacin Nigeria ta gurfanar da wani matashi mai kimanin shekaru 25 bisa zarginsa da kashe mahaifinsa ta hanyar amfani da makami.

Wani matashi ‘ya kashe mahaifinsa’ saboda aure a Jigawa

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi cikin dare yayin da mahaifin wanda ake zargin mai kimanin shekaru 65 yake bacci. Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya shaida wa BBC cewa binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa matashin ya kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa fartanya da kuma itace bisa […]