Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a London

Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wadan su gwamnonin kasar guda bakwai a yau da yamma a Abuja House dake birnin London wanda cikin har da dan jam’iyyar PDP. Ziyarar ta yau ta biyo bayan wata ziyara da wadansu gwamnonin suka kai a satin daya gabata wadanda suka hada da gwamnan jihar Kaduna Mallam […]

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Wasu mata sun gudanar da zanga-zanga kan yadda al'umma a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ke yin wasarairai da matsalar karuwar fyade.

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Aisha Dan kani ta ce sun gudanar da zanga-zangar ce don zaburas da jama’a kan alhakin da ya rataya a wuyansu na shawo kan karuwar fyade. Zanga-zangar wadda tsoffin daliban makarantar St. Louis suka shirya amma gwamnatin jihar Kano ta ce kada a yi, ta ci gaba da gudana […]

Takaddamar Tantance Mace a Matsayin Kantomar Karamar Hukuma a Kano

Takaddamar Tantance Mace a Matsayin Kantomar Karamar Hukuma a Kano

WASHINGTON D.C. — Majalisar dai ta amince da mutane 32 daga cikin 44 yayin da tayi watsi da mutane 3 saboda rashin cancantarsu, sai kuma guda 9 da ta jingine batun tantancesu sai an zurfafa bincike akansu. Hajiya Binta Fatima Yahaya, wadda ke da digiri biyu akan fasahar taswirar gine-gine, ma’aikaciyace a jami’ar kimiyya da fasaha […]

Jihar Kano Na Zaman Makokin Rasuwar Dan Masani

Jihar Kano Na Zaman Makokin Rasuwar Dan Masani

Al’ummar Jihar Kano a arewacin Najeriya na zaman makokin rashin Dattijo Alhaji Dr. Maitama Sule Dan Masanin Kano wanda ya rasu a ranar 2 ga watan Juli na 2017 a birnin Alkahira na kasar Misra bayan wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya. Marigari Dr. Maitama Sule ya kasance a yayin rayuwar sa hazikin mutum kuma mai […]

Malaman Nigeria na adawa da ‘yancin kananan hukumomi

Malaman Nigeria na adawa da ‘yancin kananan hukumomi

Kungiyar Malaman makarantar Primary ta Najeriya ta yi zanga-zanga tana neman a tsame ta daga yunkurin bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai. Mambobin kungiyar sun yi tattaki zuwa majalisar dokoki a jihar da kuma ofishin shugaban ma’aikatan jihar domin mika kokensu. Mukaddashin kungiyar reshen jihar, Comrade Dalhatu AbduSalam Sumaila ya ce `ya`yan kungiyar […]