‘An kashe ‘yan Nigeria 97 a Cameroon’

Wasu 'yan Najeriya sun ce ana gallaza musu kuma an kashen 'yan Najeriya 97 a yankin Bakassi da ya koma hannun Kamaru daga Najeriya.

‘Yan Najeriyan da suka arce daga yakin Bakassin sun yi zargin cewar jandarmomi na bin gida-gida domin karbar kudaden haraji, wanda suka ce ana tsawwala musu kuma sukan harbe wadanda suke nuna musu turjiya. A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta ce rahoton gallazawa ‘yan kasar a Kamaru ya saba wa yarjejeniyar da kasashen biyu suka […]