Hukumar EFCC Ta Bankado Miliyoyin Kudi Da Dillalan Mai Su Ka Ci

A cigaba da bankado kudaden Najeriya da wasu manyan barayi su ka sace, hukumar yaki da almundahana da gurgunta tattalin arzikin kasa (EFCC) karkashin Ibrahim Magu, ta sake gano wasu kudaden da aka yi kwana da su a bangaren mai.

Hukumar EFCC Ta Bankado Miliyoyin Kudi Da Dillalan Mai Su Ka Ci

Wakilin VOA Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko da rahoto cewa, “Jiya Talata Hukumar EFCC mai yaki da ayyukan karya tattalin arziki a Najeriya ta fadawa taron manema labarai a Kano cewa, ta kwato fiye da naira biliyan 328 daga hannun manyan kamfanonin dillancin mai guda tara a kasar da aka so yin […]