Najeriya: MDD Ta Dakatar Da Shirin Raba Abinci a Sansanin Gubio

Bayanai masu karo da juna sun nuna cewa hukumar samar da abinci ta WFP ta dakatar da ayyukan raba abinci a wani sansani da ke jihar Bornon Najeriya bayan da aka zargi 'yan gudun hijrar da kai wa ma’aikatanta hari saboda ana yawan basu tuwo babu sirki.

Najeriya: MDD Ta Dakatar Da Shirin Raba Abinci a Sansanin Gubio

Hukumar da ke kula da shirin samar da abinci ta WFP dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta dakatar da ayyukan samar da abinci ga ‘yan gudun hijra da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijra da ke Gubio a jihar Borno. Hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda far ma ma’aikatanta da ‘yan gudun hijrar […]