Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar.

Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan  wata  yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar. Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote shi da kansa ya sanya hannu a madadin kamfaninsa shi kuwa Gwamna  Abubakar Sani Bello ya sanya hannu a madadin jihar Neja. Da yake […]

Kano ta Tara Gudunmowar Biliyan 2 don Tallafawa Wadanda Annobar Gobara ta Shafa a Jihar

Kano ta Tara Gudunmowar Biliyan 2 don Tallafawa Wadanda Annobar Gobara ta Shafa a Jihar

Ranar Lahdi (20/08/2017) ne gwamnatin jihar Kano ta jagoranci tara tallafin naira biliyan biyu don tallafawa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a jihar, tare da samun gudunmowa mafi girma ta Naira Miliyan 500 daga gurin shugaban taron, Alhaji Aliko Dangote. Gwamnatin jihar ta shirya taron bada tallafin don taimakawa wadanda annobar gobara ta shafa […]

Dangote ya bawa ‘yan kasuwar Kano Naira Miliyan 500

Dangote ya bawa ‘yan kasuwar Kano Naira Miliyan 500

Shugaban gamayyar kamfanunuwan Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da bayar da gudummawar Naira Miliyan 500 ga wadanda gobarar kasuwannin Kano suka shafa a shekarar da ta gabata. Aliko Dangote ya sanar da hakan ne a yayin taron hada gudummawa ga ‘yan kasuwar a dakin taro na Coronation Hall wanda ke fadar gwamnatin jihar Kano […]

Dangote ya sayar da hannun jari mai yawa

Rukunin Kamfanonin Dangote ya sayar da hannun jari na miliyoyin daloli a kamfaninsa na siminti ga wasu masu zuba jari na kasashen waje a wani ciniki da ka iya juya akalar kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

Dangote ya sayar da hannun jari mai yawa

A ranar Talata Dangote Industries, wanda mutumin da ya fi kowa wadata a Afirka Aliko Dangote ya mallaka, ya sayar da hannun jari miliyan 416 na Dangote Cement a kan kudi naira biliyan 86, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 236. Malam Abubakar Aliyu, wani masanin tattalin arziki kuma daya daga cikin masu ruwa-da-tsaki a harkar saye […]

Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’

Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’

Hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya yi kasa a jerin masu kudin duniya inda ya fado daga mataki na 51 zuwa 105, in ji mujallar Forbes. Mujallar ta ce arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a shekarar 2016 zuwa biliyan 12.2 a bana. Hakan dai ya faru ne, a cewar […]

Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da Basarake Oba na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunlisi, sun kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin kabilun Hausawa da Yarbawa da ke garin na Ile-Ife.

Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

Zaman dai ya zo a karkashin gidauniyar Dangote da ta bayar da sama da naira miliyan 50 ga al’ummar da rikicin kabilancin tsakanin Hausawa da Yarbawa ya shafa cikin watan Maris na bana. Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote na cikin masu halartar wannan taron sasantawar, inda ya bayar da wani tallafi ga matasan. Sama da […]

Ni ban bai wa ‘yan majalisar Kano cin hanci ba – Dangote

Ni ban bai wa ‘yan majalisar Kano cin hanci ba – Dangote

Attajirin dan kasuwar da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya ce zargin bayar da cin hancin da ake masa “ba gaskiya ba ne.” A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki zargin da ake wa attajirin kan bai wa majalisar kudi don su dakatar da […]