Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

‘Yan sanda na zargin wani mutum da kashe matarsa a cikin jirgin ruwa a jihar Alaska ta Amurka saboda “ta ki daina yi masa dariya”. Ana zargin Kenneth Manzanares da laifin kisan matarsa mai shekara 39, wacce aka gano gawarta an yi mata raunuka da dama a kanta a cikin jirgin ruwan. An tsare shi […]

‘Ba mu amince da sauya fasalin Obamacare ba’

‘Ba mu amince da sauya fasalin Obamacare ba’

Majalisar dokokin Amurka tayi watsi da kudirin yi wa shirin tsohon shugaban kasar, Barack Obama na lafiya da aka fi sani da Obama Care garanbawul. Hakan ya biyo baya ne bayan wata takardama da aka shafe awanni anayi ewanda takai majalisar har izuwa karfe 2 na daren yau Juma’a. Ana ganin ba karamin cikas ya […]

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi fatali da takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wasu manyan 'yan siyasa da jami'an sojin kasarsa goma sha uku.

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Amurka dai ta ce ta dauki matakin domin nuna wa Mr. Maduro cewa da gaske take a barazanar ta yi na kakaba wa Venezuela takunkumi karya tattalin arziki cikin sauri idan ya ci gaba da shirinsa na gudanar da wata kuri’ar da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa domin kafa wata sabuwar majalisar dokoki. […]

Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Kano, Nigeria – Gwamnatin Rasha ta bukaci Amurka data dawo mata da gidajen ta na Diflomasiyya data kwace sakamakon rikicin kutse kan al’amuran zaben kasar wanda Shugaba Donald Trump ya lashe a watan Nuwamba na shekara ta dubu biyu da shida. Mai magana da yawun Fadar Klemlin Dmitry Peskov yace ba zai yiwu ba gwamnatin […]

Trump, Putin Sun Yi Ganawar Farko

A karon farko tun bayan da ya karbi ragamar mulkin Amurka, shugaba Donald Trump ya gana da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin, tattaunawar da ta mamaye taron kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a duniya dake gudana a Jamus.

Trump, Putin Sun Yi Ganawar Farko

WASHINGTON D.C. — Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sun tattauna da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin kan batutuwa da dama wadanda za su taimakawa kasashen biyu a nan gaba. “Ina da muradin ganin abubuwa masu alfanu sun faru da Amurka da Rasha.” In ji Trump a lokacin ganawarsa ta ido-da-ido ta farko da ya […]

Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka

Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke wanda ya ba shi damar hana Musulmi daga wasu kasashe shiga kasar, yana mai cewa hakan “wata nasara ce ga tsaron kasa”. Kotun kolin ta kuma amince da wani bangare na bukatar fadar White House ta hana ‘yan gudun hijira […]

‘Nigeria za ta sha gaban Amurka wajen yawan al’umma’

‘Nigeria za ta sha gaban Amurka wajen yawan al’umma’

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya a kan yawan al’ummar Duniya na shekarar 2017 ya ce Najeriya za ta sha gaban Amurka a yawan al’umma.. Haka zalika rahoton ya yi hasashen cewa kasar za ta kasance ta uku mafi yawan al’umma a duk fadin duniya nan da shekarar 2050. Rahoton wanda aka fitar a ranar […]

Jiragen Yaki: Amurka Ta Bukaci Bayani Daga Najeriya

Jiragen Yaki: Amurka Ta Bukaci Bayani Daga Najeriya

Fadar shugabana kasar Najeriya ta maida martani kan matsayin wadansu sanatocin Amurka biyu na kin amincewa da kudurin shugaba Trump na sayarwa Najeriya da jiragen yaki Sanatocin da suka hada da Cory Booker na jam’iyar Democrat da Rand Paul na jam’iyar Republican sun bayyana rashin amincewarsu da kudurin shugaba Donald Trump na amincewa a saidawa […]