Komitin Sulhu na MDD Zai Dauki Mataki Kan Korea ta Arewa Littini

Littinin nan ne Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama na musamman domin tattauna batun sake gwajin makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi, don duba irin matakin da ya dace a dauka.

Komitin Sulhu na MDD Zai Dauki Mataki Kan Korea ta Arewa Littini

Kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Japan da Korea ta Kudu suka bukaci zaman na musamman  na littini. Tun jiya lahadi Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da ayarin mashawartansa game da harkokin tsaro inda suka duba gwaji na baya-bayan nan na makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi. Sakataren Watsa labarai na Ofisshin Shugaban […]