Atiku ‘na so talakawa su karbi mulki’

Atiku ‘na so talakawa su karbi mulki’

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce yana so a sake fasalin kasar yadda talakawa za su karbi ragamar tafiyar da ita. A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon dan takarar shugaban Najeriya ya ce, “ina so a sauya tsarin kasarmu domin kwace mulki daga masu kudi zuwa mutanen […]

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta ce ba za ta iya shiga zabukan majalisun kananan hukumomi da za a yi a jihar Kebbi a yawancin wurare ba saboda karancin kudi.

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Idan an jima dai ne za a bude rumfunan zabe domin zaben shugabannin da kansiloli na kananan hukumomin jihar 21. Jam’iyyar dai ta ce ta tsayar da ‘yan takarar shugabancin ne a kananan hukumomin shida kacal. Ibrahim Umar Ummai shi ne sakataren watsa labaran ta, Sakataren yada labaran jam’iyyar ya shaidawa BBC cewa hukumar zaben […]

INEC ta dage kiranyen Melaye

Hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta dage shirin da take yi na tantance takardun neman kiranye da ta shirya za ta yi a kan dan majalisar dattawa Dino Melaye.

INEC ta dage kiranyen Melaye

Hukumar ta fitar da wannan bayanin ne bayan da ta sami umarni daga wata kotu na ta dakatar da shirin nata. Hukumar ta INEC ta ce, “A matsayinmu na hukuma mai mutunta bangaren shari’a, mun yanke shawarar bin umarnin kotu”. Amma hukumar ta ce za ta ci gaba da neman kotun ta janye umarnin, kuma […]

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho. Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a birnin London, ya yi wa Cif Akande ta’aziyya bisa ga rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande. Wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar […]

Za a fatattaki miyagu daga gwamnatin Buhari — Aisha

Za a fatattaki miyagu daga gwamnatin Buhari — Aisha

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta yi wani shagube kan al’amuran da suke faruwa a gwamnatin mijinta, tun bayan tafiyarsa jinya karo na biyu a birnin London. Ta wallafa shaguben ne a shafinta na Facebook ranar Litinin, inda ta yi amfani da abin da Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna ya rubuta yana habaici […]

Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

Hukumar zaben jihar Jigawa ta gudanar da zabe a jihar Jigawa bayan kotu ta bada umarnin a dakatar da zaben.

Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

WASHINGTON DC — Yau hukumar zaben Jigawa ke gudanar da zaben shugabannin kanananan hukumomin jihar 27 da kuma kansiloli 284 a fadin jihar. Hukumar tace Jam’iyyu 10 ne ke fafatawa a zaben, amma Jam’iyyar PDP dake zaman babbar Jam’iyyar hamayya tace ba zata shiga zaben ba saboda girmama umarnin alkalin babbar kotun tarayya dake Dutse wanda […]

‘Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari’

‘Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari’

Yawan fitar jama’a ƙwansu da kwarkwatarsu su kaɗa ƙuri’u a lokacin zaɓuka, ka iya yin tasiri wajen tausasa gwiwar ‘yan siyasa su wanzar da shugabanci nagari. Jami’in wata ƙungiya mai sa ido kan zaɓuka, Assembly For Peace ne ya yi wannan ankaraswa jim kaɗan bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin […]

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya ce babu wani bambanci tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP a kasar. Sai dai tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ta’annati (EFCC) ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki […]