Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 20 a Nigeria

Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu sannan fiye da 30 suka samu munanan raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Konduga.

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 20 a Nigeria

Wasu mata ne guda uku suka kai harin a wata kasuwar sayar da raguna da ke unguwar Mandirari da yammacin ranar Talata. An ce guda biyu daga cikin matan sun kai ga tayar da bama-baman da ke jikinsu, a inda jami’an tsaro suka harbe ta ukun kafin ta tayar da nata. Matan sun kasu gida […]