Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona

Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona

Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu na Spanish Super Cup a ranar Laraba a Santiago Bernabeu. Wasan farko da aka yi a a gasar a Nou Camp, Real ce ta yi nasara da cin kwallaye 3-1, kuma a karawar ce aka bai wa Cristiano jan kati. Wannan ne karo na […]

Zinedine Zidane zai tsawaita zamansa a Madrid

Zinedine Zidane zai tsawaita zamansa a Madrid

Zinedine Zidane ya tabbatar da cewar zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horas da Real Madrid nan bada dadewa ba. Zidane ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Asabar kan karawar da Real Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan farko na Spanish Super Cup a […]

Borussia Dortmund ta rasa inda Dembele yake

Borussia Dortmund ta rasa inda Dembele yake

Kociyan Borussia Dortmund ya ce dan wasansu da Barcelona ke nema fafurfafur Ousmane Dembele, domin maye gurbin Neymar bai halarci atisayen kungiyar ta Jamus ba a yau Alhamis. Peter Bosz ya ce kungiyar ta Bundesliga ta kasa samun wani bayani ko ji daga dan wasan na gaba na Faransa mai shekara 20. Kociyan ya ce […]

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17. Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi. Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da […]

‘Neymar, Sanchez da Matic za su sauya kulob’

Dan wasan gaban Barcelona Neymar ya shaida wa takwarorinsa a kulob din cewa zai koma Paris St-Germain (PSG) kan fam miliyan 196, in ji jaridar Le Parisen ta Faransa.

‘Neymar, Sanchez da Matic za su sauya kulob’

Sai dai kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce maganar “jita-jita ce kawai” kuma suna so dan wasan ya ci gaba da kasance da su, kamar yadda jaridar Metro ta ruwaito. Jaridar Mundo Deportivo a Spain ta ruwaito cewa Barcelona na son sayen dan wasan Juventus Paulo Dybala idan Neymar ya tafi. Manchester City ta amince […]

Barcelona ta sake sayan Gerard Deulofeu daga Everton

Barcelona ta sake sayan Gerard Deulofeu daga Everton

Barcelona ta sake sayan dan wasan gefe Gerard Deulofeu daga Everton bisa wata yarjejeniyar da ake ganin ta kai fam miliyan 10.6. Da farko Deulofeu ya je Everton ne kan aro a kakar 2013-2014, sannan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar din-dindin a shekarar 2015. Dan wasan mai shekara 23 ya buga wa Everton wasanni 13 […]

Messi zai biya tara maimakon zaman gidan yari

Messi zai biya tara maimakon zaman gidan yari

Akwai yiwuwar shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi zai kaucewa daurin wata 21 a gidan yari inda ya zabi ya biya tara, kamar yadda rahotanni daga kasar Spain suka bayyana. Wata kotu ce a Spain ta samu dan wasan da laifin zambar haraji. Babban mai gabatar da karar kasar zai musanyawa Messi zaman gidan yari […]