Bama Bukatar Wani Sabon Yakin – Ohanaeze Ndigbo

Bama Bukatar Wani Sabon Yakin – Ohanaeze Ndigbo

Shugaban Kungiyar Igbo Zalla wato Ohanaeze Ndigbo na Kasa,  Mr. John Nwodo, yayi kira ga ‘yan Nigeriya daga kowacce kabila, addini ko nahiya da su zauna lafiya. Inda yake cewa kasar bata bukatar shiga wani yaki daban. Mr Nwodo yayi wannan maganar ne a Gombe yayin da ya jagoranci shugabannin kabilar Igbo na daukacin arewacin […]

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation Python Dance II.

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Wata sanarwar da darakatan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya sanya wa hannu, ta ce kayayyakin aikin da sojin saman Najeriya ta tura wa jami’an aikinta na musamman a Fatakwal sun hada da jirgin yaki kirar Alpha Jet. Sanarwar ta kara da cewar an tura jirgin yankin ne domin a samar […]

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai ‘Yan IPOB 67 Kurkuku

Wata babbar kotun Najeriya da ke kudu maso gabashin kasar ta bayar da umarnin kai a kalla mutum 67 'yan kungiyar IPOB gidan yari, kan zarginsu da hannu a tashin hankali na fafatukar kafa kasar Biafra.

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai ‘Yan IPOB 67 Kurkuku

Sojoji sun kama yawancin mutanen da ake zargi da kasancewa ‘yan kungiyar IPOB ne kusa da Isiala Ngwa, yayin da ‘yan sanda suka kama mutum bakwai da zargin kona ofishin ‘yan sanda na Ariara da ke Aba, wata cibiyar kasuwanci a kudu maso yammacin kasar. Mutanen sun musanta zargin da ake yi musu. Sojin Najeriya […]

Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Rundunar Sojin Nigeriya ta fara janye jam’anta a hankali wadanda ta girke a wuraren duba ababan hawa a garin Aba bayan fadan da aka gwabza da masu zanga-zangar kafa Kasar Biyafara (IPOB) Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya wato NAN ya rawaito ranar Lahdi Gwamna Okezie Ikpeazu na fadawa manema labarai a Umuahia cewa an janye sojojin […]

‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Adamawa Sunyi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addancin Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Ta IPOB A Kudu Maso Gabashin Kasar

‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Adamawa Sunyi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addancin Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Ta IPOB A Kudu Maso Gabashin Kasar

Lokacin da yake zantawa da Manema Labarai a Yola ranar Jumma’a bayan wani taro da mambobin Majalisar Tsaro ta Jihar, shugaban Cibiyar Al’adun Igbo a Jihar Adamawa Cif Obonna Paul Ibere ya zargi kungiyar ta IPOB da yunkurin kawo rikici a yankin kudu masu gabashi kasar. “Duk wanda aka samu da aikata laifin da ya […]

‘Yan Biafra ‘yan ta’adda ne — Sojin Nigeria

‘Yan Biafra ‘yan ta’adda ne — Sojin Nigeria

Rundunar sojin Najeriya ta ayyana madugun kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra da magoya bayansa a matsayin ‘yan ta’adda. Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar tsaron kasar Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce kungiyar, “ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar”. Ta kara da cewa, “Bayan mun […]

Nnamdi Kanu ya bata

Nnamdi Kanu ya bata

Rahotanni na nuna cewa madugun kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da iyayensa sun bata. Hakan na faruwa ne bayan sojoji sun kai samame gidansa a kauyen Afaraukwu da ke jihar Abia da ke kudu maso gabashin kasar ranar Alhamis da maraice. Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya […]

Kashe Nnamdi Kanu sojin Nigeria suka zo yi – Bar Ejiofor

Kashe Nnamdi Kanu sojin Nigeria suka zo yi – Bar Ejiofor

Lauyan jagoran kungiyar masu rajin kafa Biafra a Najeriya, Barista Ifeanyi Ejiofor ya zargi rundunar sojin kasar da yunkurin kashe Mazi Nnamdi Kanu a gidansa. Ya ce kungiyar za ta kai kara gaban kotu don bin kadin jinin ‘ya’yanta da ‘aka ritsa da su a wannan samame na babu gaira babu dalili.’ Sai dai, mai […]

Ana ci Gaba Da Samun Raayoyi Mabanbanta Game Da Sake Kame Nnamdi Kanu.

Har yanzu a jihohin kudu maso yammacin Najeriya ana ci gaba da samun cece kuce game da batun shirin sake kame shugaban kungiyar neman sabuwar kasar Biafra wato Nnamdi Kanu

Ana ci Gaba Da Samun Raayoyi Mabanbanta Game Da Sake Kame Nnamdi Kanu.

Batun sake kame shugaban kungiyar samar da sabuwar kasar Biafra ta IPOB, wato Nnamdi Kanu naci gaba da kawo rarrabuwar kawuna a jihohin kudu maso gabashin Najeriya. Yunkurin sake kame Kanu din ya biyo bayan karya dukkan sharuddan da kotu ta gitta masa ne gabanin bada belin sa. Wani daga cikin masu raayin kafa wannan […]

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Daga Sokoto- Maigirma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar ya ce duk wanda yake da shirin kaiwa ‘yan kabilar Igbo mazauna arewacin kasar hari, to shi yakamata ya fara kaiwa wannan harin. Sarkin musulmin ya fadi haka ne lokacin da shugaban kabilar Igbon ta duniya, Dr Mishack Nnanta tare da rakiyar shugabannin kabilar Igbo mazuna yankin suka […]

1 2 3