‘Rashin ilimin mata ne silar yawan mutuwar aure’

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Bilkisu Funtua ta bayyana rashin wayewa da karancin ilimi daga bangaren mata a dalilan da ke jawo mace-macen aure a arewacin Najeriya.

‘Rashin ilimin mata ne silar yawan mutuwar aure’

Fittaciyar marubuciyar ta bayyana hakan ne a wata hirar da ta yi da sashen Hausa na BBC. Marubuciyar wadda aka fi sani da Anti Bilki ta ce ta fara rubutu ne domin samar da mafita ga matsalolin mutuwar aure a arewacin Najeriya. Duk da cewa babu alkaluma a hukumance, amma an yi kiyasin cewa arewacin […]