Shugaba Muhammadu Buhari Ya Koma Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Koma Najeriya

Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida. Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan. Amma a baya shugaban ya fi zuwa can don duba lafiyarsa. Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka. Kafin tafiyarsa, shugaban […]

Sunan Muhammad Ya Samu Matsayi A Birtaniya

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa 'ya'yansu a yanzu.

Sunan Muhammad Ya Samu Matsayi A Birtaniya

Sunan na Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini, a yanzu ya kawar da sunan William ya hau gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara. A alkaluman da hukumar ta fitar ta ce sunan Oliver wanda shi ne na daya cikin sunayen […]

‘Yan Kasashen Turai Sun Samu Sakon Su Fice Birtaniya

Kasar Birtaniya ta nemi gafarar wasu ‘yan kasashen Turai sama da 100 da suka samu sakon su fice daga kasar akan abin da ta kira kuskure. Matakin ya razana 'yan kasashen Turai da dama da suka samu sakon.

‘Yan Kasashen Turai Sun Samu Sakon Su Fice Birtaniya

Ma’aikatar cikin gidan Birtaniya ta ce ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi wasiku sama da 100 suka isa wajen ‘yan kasashen Turai da ke zama a kasar. Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan ta bayyana cewar lallai an samu kuskure wajen aikawa da wasikun, kuma suna tuntubar duk wadanda suka samu wasikar […]

Shugaba Buhari Zai Koma Bakin Aikinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya aike wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar, inda yake sanar da ita cewa zai koma bakin aikinsa, bayan dawowarsa daga hutun jinya da ya yi a Birtaniya.

Shugaba Buhari Zai Koma Bakin Aikinsa

Shugaba Buhari ya koma Najeriya ne ranar Asabar 19 ga watan Agusta, kuma a wasikar da ya rubuta wa majalisar dattijai da ta wakilan kasar, ya shaida musu cewa zai koma bakin aikin nasa ne a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce, […]

Marasa Dattako Ke Kalaman Kiyayya – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar kasar jawabi a safiyar ranar Litinin kwana biyu bayan komawarsa kasar.

Marasa Dattako Ke Kalaman Kiyayya – Buhari

A jawabin mai tsawon minti 5.40, shugaban ya yi godiya ga ‘yan kasar bisa ga addu’o’in da suka yi masa yayin da shafe kwana 103 yana jinya a birnin Landan. Har ila yau shugaban ya mayar da martani ga masu fufutikar ballewa daga kasar da batun tsaro da kuma gyara tattalin arzikin kasar. Sai dai […]

Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.

Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki. Ya bayyana cewa yana ci gaba da murmurewa da samun koshin lafiya kuma yana bukatar ya dawo gida. “Amma yanzu na […]

Nigeria: Kun san yadda Biafra ta samo asali?

Biafra wata kalma ce da masu fafutikar ballewa daga Najeriya a yankin Kudu maso Gabashin kasar suke amfani da ita wajen bayyana fatansu na ganin sun kafa kasar kansu wadda su kai wa lakabi da "Jamhuriyar Biafra".

Nigeria: Kun san yadda Biafra ta samo asali?

Sunan Biafra ya samo asali ne da gabar mashigin tekun Atlantic da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar. Galibi mutanen da suke zaune a yankin ‘yan kabilar Igbo ne amma akwai wasu kabilu kamar Efik da Ibibio da Annang da Ejagham da Eket da Ibeno da kuma Ijaw. Kokarin ballewar yankin daga Najeriya shi ne […]

”Yan Nigeria na cikin wadanda aka fi bautarwa a Birtaniya’

Hukumomin tsaro a Birtaniya sun ce girman matsalar bauta ta zamanin da ake yi a kasar ta fi yadda ake tsammani a baya.

”Yan Nigeria na cikin wadanda aka fi bautarwa a Birtaniya’

Hukumar kula da manyan laifuka ta kasar, NCA, ta ce, adadin da ake da shi a baya na mutanen da ake bautarwa ko tilastawa aiki dubu 13 kadan ne a cikin adadin da ake da shi, inda ake samun su a ko wanne manyan garuruwa da birni a Birtaniya. Mafi yawan wadanda aka fi bautarwa […]

Buhari bai saba wata doka ba saboda jinyar da yake yi a Birtaniya-Majalisa

Majalisar Dattawa jiya ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai karya doka ba saboda dadewar da ya yi ba ya kan aiki sakamakon jinyar da yake yi a kasar Birtaniya.

Buhari bai saba wata doka ba saboda jinyar da yake yi a Birtaniya-Majalisa

Majalisar Dattawa jiya ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai karya doka ba saboda dadewar da ya yi ba ya kan aiki sakamakon jinyar da yake yi a kasar Birtaniya. Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wasu kungiyoyi sun gudanar da zanga-zangar neman shugaban kasar ya dawo kan aiki ko kuma ya yi murabus. A wata […]

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho. Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a birnin London, ya yi wa Cif Akande ta’aziyya bisa ga rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande. Wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar […]