Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye

Shugaban Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya bawa Operation Lafiya Dole wa'adin kwanaki 40 ta kawo masa Shekau a mace ko a raye.

Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye

A ranar juma’a 21, ga watan yuli, shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya umurci shugaban rundunar dake yaki da boko haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru wa’adin kwanaki arba’in ya kawo masa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau a mace ko a raye. Mai magana da yawun rundunar […]

Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gargadi jama'a game da sabon salon da kungiyar Boko Haram ta bullo da shi wajen kai hare-haren kunar bakin wake kan gine-ginen gwamnati.

Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar, Victor Isuku ya shaida wa BBC cewa kananan yaran na kiwo ne a wani daji lokacin da ‘yan Boko Haram din suka daura musu damarar bama-baman tare da gargadinsu kada su kwance har sai sun isa gida. Ya kuma kara da cewa, ”An daura wa Gambo Bukar […]

Najeriya ta karbi Jirayen Yaki 5 daga Pakistan

Najeriya ta karbi Jirayen Yaki 5 daga Pakistan

Rundunar Sojin saman Najeriya ta karbi wasu sabbin jiragen yaki guda biyar. Wani katon jirgin dakon kaya ya sauka a tsohon filin sauka da tashin jiragen sama na Soji dake jihar Kaduna. Jirgin wanda ya sauka da sanyin safiya na dauke da jiragen yakin da gwamnatin Najeriya ta yi odarsu daga kasar Pakistan domin ci […]

‘An kashe ‘yan Nigeria 97 a Cameroon’

Wasu 'yan Najeriya sun ce ana gallaza musu kuma an kashen 'yan Najeriya 97 a yankin Bakassi da ya koma hannun Kamaru daga Najeriya.

‘Yan Najeriyan da suka arce daga yakin Bakassin sun yi zargin cewar jandarmomi na bin gida-gida domin karbar kudaden haraji, wanda suka ce ana tsawwala musu kuma sukan harbe wadanda suke nuna musu turjiya. A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta ce rahoton gallazawa ‘yan kasar a Kamaru ya saba wa yarjejeniyar da kasashen biyu suka […]

Yadda Wasu ‘Yan Boko Haram Suka Gudo Suka Mika Kansu

Ana ci gaba da samun bayanai masu ingancin kan yadda wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram su 70 suka gujewa sansaninsu suka ajiye makamansu tare da mika wuya a garin Maiduguri dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Yadda Wasu ‘Yan Boko Haram Suka Gudo Suka Mika Kansu

WASHINGTON D.C. — Bayanai daga ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da suka tsere suka kuma mika kansu ga jami’an tsaro, sun yi nuni da cewa mutanen sun sulale ne daga sansanoninsu ba tare da sanin shugabanninsu ba, inda suka yi ta tafiya daga wani gari zuwa gari kafin har su kai Maiduguri. “Sun yi tafiya ne daga […]

An sake kai hari Jami’ar Maiduguri

An sake kai hari Jami’ar Maiduguri

Rahotanni dake fitowa daga birnin Maiduguri na Jihar Borno, na cewa ‘yan kunar bakin wake sun sake afkawa cikin Jami’ar Maiduguri, inda biyu daga cikinsu suka tashi wani abu mai fashewa dake jikinsu. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na daren Alhamis, a inda wasu da suka shaida lamarin sun ce wasu mutane […]

Ibrahim Magu: ‘A rika daure barayin gwamnati a dajin Sambisa’

Ibrahim Magu: ‘A rika daure barayin gwamnati a dajin Sambisa’

Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya yi kira da a kafa kurkuku a dajin Sambisa domin a rika tsare wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar. Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da ake bikin bude sabon ofishin shiyya na hukumar a Kaduna […]

Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

Mayakan kungiyar Boko Haram 700 ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya, kamar yadda rundunar sojojin kasar ta yi ikirari. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce mika wuyan ya biyo bayan farmakin da dakarun Najeriya suka kai ranar Litinin. Har ila yau, Kukasheka […]