Majalisa tana neman rage karfin shugaban kasa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kuduri da ke neman rage karfin shugaban kasar wajen tsarawa da kuma amincewa da doka.

Majalisa tana neman rage karfin shugaban kasa

‘Yan majalisar sun amince a ragewa shugaban kasar karfin ikonsa na hawa kujerar na ki kan kudurin dokokin da majalisar ke tsarawa, a wani bangare na gyaran da suke yi wa tsarin mulkin kasar. Masu sharhi na ganin majalisar na kokarin rage ikon da shugaban kasa ya ke da shi da kuma mayar da shi […]

Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami’anta

Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada matsayinta na cewa ba za ta sake tantance sunan kowa da Fadar shugaban kasa za ta gabatar ba har sai ta cika wasu sharudda da suka hada da amincewa da cewa ita ke da hurumin tantance jami'an da za a nada a mukamai.

Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami’anta

Majalisar wacce ta nuna rashin jin dadinta kan kin cire Ibrahim Magu duk da cewa ta taki tabbatar mai da mukaminsa, a baya-bayan nan ta ki tantance Mr Lanre Gbajabiamila da bangaren zartaswar ya mika mata. Daga cikin sharuddan da majalisar akwai batun sai mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya amince cewa majalisar na […]