Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

An fara kwaso yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, bayan sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, da nufin hada su da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

Wasu daga cikin yaran dai marayu ne yayin da wasu kuma har yanzu iyayensu na nan da rai kuma an kwaso su ne cikin jirgin sama, wasu daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minaoa. Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ce ta dauki gabarar wannan aiki na sada irin wadannan yara da iyaye ko […]

Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama dake jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da ‘ya’yansa biyar, a cikin shekaru 4 da suka gabata. Ya dai nemi sakaya sunansa saboda matsalar tsaro. Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa […]

Za a fara yin shari’ar ‘yan Boko Haram 1,600

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya don gurfanar da mutanen da ake tuhuma da zama mayakan kungiyar Boko Haram sama da 1,600 a gaban kotu.

Za a fara yin shari’ar ‘yan Boko Haram 1,600

Ministan Shari’a na kasar Barista Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a fara yi wa mutanen shari’a ne a cibiyoyi daban-daban da ake tsare da su daga watan gobe. Ma’aikatar shair’ar ta kara da cewa an bayar da shawarar sakin mutane 220 da ake zargi da zama ‘yan Boko Haram saboda babu wata […]

Nigeria Ce Ta Daya a Yaran Da Basa Zuwa Makaranta — UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kasashen Afrika su ne suka fi fama da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.

Nigeria Ce Ta Daya a Yaran Da Basa Zuwa Makaranta — UNICEF

Asusun ya ce, Najeriya kuma, ita ce ta fi yaran da ba sa zuwa makarantar a tsakanin kasashem duniya gaba daya. Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna cewa, kashi 46 cikin 100 na yara a Najeriya, ba sa zuwa makarantar gaba da firamare wato sakandire, wanda wannan adadin shi ne kusan […]

‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 15 A Borno

‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 15 A Borno

‘Yan kunar bakin waken da ba asan ku su wanene ba sun kashe a kalla mutum 15 a Arewa masu Gabashin Kasar Nijeriya kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito, inda suka zanta da ma’aikatan ceto da ‘ya sintiri. An dai ce harin ya faru ne a Konduga, wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar […]

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Wani dan kungiyar Boko Haram da ake kira da kwamanda a tsakanin ’ya’yan kungiyar, ya yi ikirarin cewa shi ne ya jagoranci sace ’yan matan Chibok daga makaranta a shekarar 2014. ‘Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar labarai ta PRNigeria. Fiye […]

kwamanda na Boko Haram ya mika wuya a Jihar Borno

Sojojin sunce a na bincikan kwamandan na Boko Haram har ya furta gaskiya cewa yana daya daga cikin wadanda suka kai hari jihar Adamawa a garin Madagali da kuma sauran jihohi na arewa ta gabas inda suka kashe matasa da yawa.

kwamanda na Boko Haram ya mika wuya a Jihar Borno

Daya daga cikin manyan Kwamandoji na Boko Haram mai suna Auwal Isma’il ya mika wuya ga sojojin Najeriya da suke aiki a yankin jihar Borno.   Isma’il ya sanar da jami’an tsaron cewar shi babban ma’aikaci ne a kungiyar ta Boko Haram inda ya taka babbar rawa, ya kara da cewa yana daya daga cikin […]

Amurka Ta Saidawa Najeriya Jiragen Yaki 12

Ma’aikatar tsaron Amurka ta shaidawa Majalisar kasar saidawa Najeriya jiragen sama na yaki 12, da kuma sauran makaman da kudin su ya kai Dala miliyan 593, domin amfani da su wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Amurka Ta Saidawa Najeriya Jiragen Yaki 12

Ma’aikatar tsaron Amurka ta shaidawa Majalisar kasar saidawa Najeriya jiragen sama na yaki 12, da kuma sauran makaman da kudin su ya kai Dala miliyan 593, domin amfani da su wajen yaki da kungiyar Boko Haram. Ofishin hadin kan tsaro na Amurka, yace cinikin ya kunshi tarin bama bamai da makaman roka wanda tsohuwar gwamnatin […]

Najeriya: MDD Ta Dakatar Da Shirin Raba Abinci a Sansanin Gubio

Bayanai masu karo da juna sun nuna cewa hukumar samar da abinci ta WFP ta dakatar da ayyukan raba abinci a wani sansani da ke jihar Bornon Najeriya bayan da aka zargi 'yan gudun hijrar da kai wa ma’aikatanta hari saboda ana yawan basu tuwo babu sirki.

Najeriya: MDD Ta Dakatar Da Shirin Raba Abinci a Sansanin Gubio

Hukumar da ke kula da shirin samar da abinci ta WFP dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta dakatar da ayyukan samar da abinci ga ‘yan gudun hijra da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijra da ke Gubio a jihar Borno. Hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda far ma ma’aikatanta da ‘yan gudun hijrar […]

Fyade: Iyaye na Ficewa Da ‘Yayansu a Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Ana zargin Jami'an tsaro da 'yan kato da gora da yi wa mata fyade a sansanonin 'Yan gudun hijira

Fyade: Iyaye na Ficewa Da ‘Yayansu a Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira a Maiduguri

An samu karuwar zargin fyade a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri jihar Borno, abinda ya tilastawa wasu mutane ficewa daga sansanonin domin kare ‘ya’yansu, kamar yadda wakilin RFI a Maiduguri Bilyaminu Yusuf ya aiko da rahoto. AFP