Ba zan sauka daga mukamina ba — Bukola Saraki

Ba zan sauka daga mukamina ba — Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Satana Bukola Saraki ya bayyana cewa yana nan daram akan kujerar sa ta mulki ba. A jawabin da ya yi wa manema labarai a yau Laraba bayan hatsaniyar da aka samu a majalisar dokokin Najeriya a jiya Talata, Sanata Bukola Saraki ya ce zaben shi aka yi kafin ya samu kujerar, […]

Shugaba Buhari ya nemi gafarar ‘yan majalisa kan hana su ganinsa

Shugaba Buhari ya nemi gafarar ‘yan majalisa kan hana su ganinsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar shugabannin majalisar dokokin Najeriya bisa hana su shiga fadarsa da jami’an tsaro suka yi a ranar Alhamis da daddare. Jami’an tsaron fadar sun hana shugabannin majalisar shiga ne bisa dalilin cewa ba a ba su izinin barin su ba, suka kuma bukaci sai sun sauko daga motar safa da […]

IPOB: Sanatoci Zasu Gana Da Shugabannin Tsaron Kasa

IPOB: Sanatoci Zasu Gana Da Shugabannin Tsaron Kasa

Daga Abuja – Shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa, Dr Bukola Saraki yace majalisar zata gana da Shugabannin Tsaron Kasar nan don tsara hanyar magance rikice-rikicen da suka haifar da tashin hankali a Kudu Masu Gabashin Kasar. Yace ana tsammanin ganawar nan bada dadewa ba, haka kuma ganawar zata maida hankali kan tashin hankalin da ke […]

Buhari yana samun sauki – Yakubu Dogara

Buhari yana samun sauki – Yakubu Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa jikin shugaba Muhammadu Buhari yana murmurewa sosai. Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Rt. Hon. Yakubu Dogara tare da Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa Bukola Saraki sun ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a gidan Abuja dake birnin Landan a yau Alhamis din nan. President @MBuhari […]

‘Yan Najeriya Na Mayar da Martani Kan Kafa Dokar Hana Kalamun Batanci

A cikin wata sanarwa jiya shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya ce zasu mayar da hankali wajen kafa dokar hana kalamun batanci da dokar hana mutane aiwatar da shari'a da kansu maimakon su bar kotu ta yanke hukumci.

‘Yan Najeriya Na Mayar da Martani Kan Kafa Dokar Hana Kalamun Batanci

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya fada cikin wata sanarwa jiya cewa kudurorin hana kalamun batanci da na daukan hukumci a hannu zasu sami kulawar da ta kamata domin su zama dokoki cikin karamin lokaci. Inji Sanata Saraki hakan nada nasaba da yadda kalamai da lafuza dake kara dumama yanayi ke ci gaba […]

Na dade da daina karbar kudin fansho daga Kwara – Saraki

Na dade da daina karbar kudin fansho daga Kwara – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Ta Kasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewar ya dade da daina karbar kudin fanshonsa a matsayinsa na tsohon gwamna daga jira Kwara. Shugaban ya haryana hakan ne a wajen wani taro na kamfanin dillacin labarai na kasa wato (NAN). Saraki, ya kara da cewa ya rubuta wasika cewar gwamnati ta […]

Zamu tabbatar harkar lafiya ta samu isassun kudi a 2018 – Saraki

Zamu tabbatar harkar lafiya ta samu isassun kudi a 2018 – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dakta Bukola Saraki ya bayyana cewa Majalisar Dattawan zata yi iya bakin kokarin don ganin cewar fannin lafiya ya samu isassun kudade a kasafin kudin badi. Shugaban ya ambata hakan a lokacin bude taron karawa juna ilimi akan harkar lafiya a bangaren zartaswa. Shugaban ya kara da cewa ya umarci ministan […]

Nigeria ta daukaka kara kan wanke Bukola Saraki

Nigeria ta daukaka kara kan wanke Bukola Saraki

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a daukaka kara a kan wanke shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki daga zargin kin bayyana kadarorinsa. Kuma a ranar Talata ne gwamnatin ta shigar da karar a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin kasar. Mista Malami ya kuma jaddada aniyar […]

Kotu ta wanke Saraki kan kin bayyana kadarorinsa

Kotu ta wanke Saraki kan kin bayyana kadarorinsa

Kotun kula da da’ar ma’aikata ta Najeriya ta yi watsi da karar da ke gabanta wadda ake tuhumar shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da laifin kin bayyana kadarorinsa. A lokacin da yake yanke hukunci, Babban alkalin kotun daukaka karar Danladi Umar, ya ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjoji […]