Tiemoue Bakayoko ya koma Chelsea daga Monaco

Tiemoue Bakayoko ya koma Chelsea daga Monaco

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiyar kulob din Monaco a kan fam miliyan 40. Ya kulla yarjejeniya shekara biyar ne da zakarun firimiyan. Dan wansan tawagar Faransar shi ne dan kwallo na biyu da Chelsea ta saya a kakar bana bayan ta sayi Antonio Rudiger daga Roma. Bakayoko ya koma Monoco […]

Za a gwada lafiyar Lukaku a Man United

Za a gwada lafiyar Lukaku a Man United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta yi gwajin lafiyar Romelu Lukaku bayan ta kammala cinikinsa a kan fam miliyan 75 daga Everton. Man U ta bayyana cewa tana farin ciki da sayen dan wasan kuma za a kammala kulla yarjeniyar ne bayan gwajin lafiyar dan wasan mai shekara 24 da haihuwa. A da […]

John Terry ya yi watsi da ‘yan Premier ya koma Aston Villa

Tsohon kyaftin din Chelsea da Ingila John Terry ya yi watsi da tayin kungiyoyin Premier don ya martaba Chelsea, ya koma Aston Villa, tsawon shekara daya.

John Terry ya yi watsi da ‘yan Premier ya koma Aston Villa

Dan wasan na baya mai shekara 36, wanda kwantiraginsa a Stamford Bridge ta kare ranar 30 ga watan Yuni ya koma kungiyar ta Chamionship ne saboda ba ya son ya je wata kungiya ta Premier wanda hakan zai sa ya kara a wasa da Chelsea. Terry ya yi wa Ingila wasa sau 78, sannan ya […]

Willy Caballero: Chelsea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City

Willy Caballero: Chelsea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City

Zakarun gasar Firimiya Chelasea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City, Willy Caballero. An sallami dan asalin kasar Ajentinan ne a lokacin da kontiginsa ya kare a karshen watan Yuni. Caballero, mai shekara 35, ya je Ingila ne daga Malaga a shekarar 2014 kuma ya buga wasanni 26wa kungiyar Pep Guardiola a kakar bara. […]

Bertrand Traore ya koma Lyon a kan fam 8.8m

Bertrand Traore ya koma Lyon a kan fam 8.8m

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Bertrand Traore, ya koma kulob din Lyon a kan fam miliyan takwas da dubu 800. Traore, mai shekara 21, wanda dan asalin kasar Burkina Faso ne ya yi kakar bara ne a kulob din Ajax a matsayin aro. Ya koma Chelsea ne a shekarar 2014 kuma ya […]

Chelsea na daf da sayen Bakayoko daga Monaco

Chelsea na daf da sayen Bakayoko daga Monaco

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana daf da sayen dan wasan tsakiyar kulob din Monaco Tiemoue Bakayoko. Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce dan wasan mai shekara 22 zai taka muhimmiyar rawa a kulob din Chelsea. Maganar sayen dan wasan ta yi nisa wanda zai zama dan wasa na farko da zakarun firimiyar za su […]