World Cup: Argentina Na Ci Gaba Da Fafutika

Argentina ta ci gaba da fafutikar ganin ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 inda ta sha da kyar a hannun Venezuela, wacce ke mataki na karshe, da ci 1-1 a wasan da suka yi a gidan Argentinar.

World Cup: Argentina Na Ci Gaba Da Fafutika

Dan wasan Venezuela Jhon Murillo ya soma jefa kwallo a ragar Argentina ko da yake kwallon da suka ci kansu bayan komawa daga hutun rabin lokaci ta sa Argentina ta samu maki daya. Yanzu dai Argentina na matsayi na biyar a cikin kasashen da ke Kudancin Amurka kuma suna da sauran wasa biyu yayin da […]