Messi, Ronaldo na cikin fitattun ‘yan wasa na duniya na 2017

Messi, Ronaldo na cikin fitattun ‘yan wasa na duniya na 2017

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar sunayen wadanda za a zabi fitaccen ‘yan kwallo na duniya daga cikin su, wadanda suka hada da Cristiano Ronaldo daga Real Madrid da Lionel Messi daga Barcelona da kuma Neymar daga Paris St-Germain. A bara ma Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa, bayan da ya […]

Ronaldo Ya Kammala Hutun Dole

Mai horar da kungiyar Zinaden Zidane ya bayyana fatan Ronaldon ba zai sake fuskantar irin wannan hukunci mai tsauri ba.

Ronaldo Ya Kammala Hutun Dole

Cristiano Ronaldo zai haska a wasan da Real Madrid zata fafata da Real Betis a gobe Laraba, bayan kammala wa’adin da aka deba masa na haramcin wasanni 5 a gasar La-liga, wanda hukunci ne bisa samunsa da laifin hankade alkalin wasa a fafatawar da suka yi da Barcelona, a gasar Super Cup, wanda Madrid din […]

Madrid ta fara kare kambunta da nasara

Madrid ta fara kare kambunta da nasara

Real Madrid mai rike da kofin Zakarun Turai ta fara kare kambunta da kafar dama, bayan da ta ci Apoel Nicosia 3-0 a karawar da suka yi a wasan rukuni na takwas a ranar Laraba. Real mai kofin zakarun Turai 12 jumulla ta fara cin kwallo ta hannun Cristiano Ronaldo tun kan a je hutu, […]

An Gayyaci ‘Yan Madrid 17 Tawagar Kasashensu

Kimanin 'yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da na 'yan kasa da shekara 21.

An Gayyaci ‘Yan Madrid 17 Tawagar Kasashensu

‘Yan wasan da za su buga wa kasashensu fafatawar shiga gasar kofin duniya sun hada da Marco Asensio da Dani Carvajal da Isco da Nacho da Sergio Ramos da Lucas Vazquez. Sauran sun hada da Cristiano Ronaldo da Luka Modric da Mateo Kovacic da Keylor Navas da Gareth Bale da Casemiro da Marcelo da Toni […]

Jadawalin Fifa: Brazil ta doke Jamus

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta fitar da jerin sunayen kasashen da suka fi fice a kwallon kafa na watan Agusta, inda Brazil ta kawar da zakarun duniya Jamus a matsayi na daya.

Jadawalin Fifa: Brazil ta doke Jamus

Kasar Lionel Messi Argentina ta ci gaba da zama a gurbinta na baya, wato matsayi na uku, yayin da Switzerland ta zama ta hudu, sannan kuma Poland ta maye matsayi na biyar, matsayin da kasashen biyu ba su taba kaiwa ba. Portugal din Cristiano Ronaldo ta rufto daga matsayi na hudu zuwa na shida, amma […]

Ronaldo ya koma atisaye a Real Madrid

Ronaldo ya koma atisaye a Real Madrid

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da ‘yan wasan Real Madrid domin tunkarar wasannin bana. Ronaldo wanda ya lashe kofin Zakarun Turai da na La Liga a Madrid a kakar da ta kare, ya kammala hutun da kungiyar ta amince ya yi, bayan da ya buga wa Portugal […]

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17. Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi. Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da […]

Ba za mu yi kasadar neman Ronaldo ba – Mourinho

Ba za mu yi kasadar neman Ronaldo ba – Mourinho

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ba sa neman Cristiano Ronaldo ya dawo kulob din daga Real Madrid. A watan Yuni ne BBC ta ruwaito cewa dan wasan yana son barin Spain saboda zarginsa da ake masa na zambar haraji. A baya ana ganin kamar akwai yiwuwar ya koma United wadda ya bari a […]

Ronaldo ya tabbatar da samun tagwaye bayan an doke Portugal

Ronaldo ya tabbatar da samun tagwaye bayan an doke Portugal

Sa’o’i kadan bayan da Chile ta fitar da Portugal daga gasar cin kofin zakarun nahiyoyi a wasan kusa da karshe a Rasha, Cristiano Ronaldo ya sanar da cewa an haifar masa tagwaye. Tsawon kwanaki kafafen watsa labarai na Portugal sun bayar da rahoton cewa wata mata da aka sanya wa cikin tayin ‘yan tagwayen a […]

Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0

Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0

Chile ta yi waje da Portugal a wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun nahiyoyi da ci 3-0 a bugun fanareti a gasar da ake yi a Rasha. Bayan minti 90 da kuma karin minti 30 na fitar da gwani, ba kasar da ta zura kwallo, hakan ya sa aka je bugun fanareti. Chile […]