‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Gwamnatin Chadi ta bayyana mamaki kan yadda Amurka ta sanya kasar cikin jerin sunayen kasashen da aka hana baki zuwa Amurka, a sabuwar dokar shugaba Donald Trump.

‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Madeleine Alingue, mai Magana da yawun gwamnatin Chadi, tace matakin yaci karo da kokarin Chadi na yaki da ta’addanci musamman a yankin Afirka ta Yamma da kuma duniya baki daya. Gwamnatin Chadi ta bukaci shugaba Donald Trump da ya sake nazari kan matakin wanda tace ya shafi kimar Chadi da kuma dangantakar kasashen biyu. Karkashin […]

America Ta Hana ‘Yan Chadi Shiga Kasarta

Shugaba Donald Trump na sanya sabon tarnakin shiga Amurka a kan kasa takwas ciki har da a karon farko Chadi da Koriya Ta Arewa da Venezuela.

America Ta Hana ‘Yan Chadi Shiga Kasarta

Haramcin ya biyo bayan bitar harkokin tsaro da kuma nasarar da umarninsa na ainihi wanda wa’adinsa zai kare ya cim ma. Shugaba Trump ya ce yana ba da fifiko wajen mayar da Amurka, kasa mai aminci. Tasirin dokokin dai ya sha bamban daga wannan kasa zuwa waccan, inda suke haramta wa ‘yan Syria da Koriya […]

Iran ta yi gwajin sabon makami mai linzami

Iran ta yi gwajin sabon makami mai linzami

Iran ta ce ta yi nasarar gwada sabon makaminta mai linzami kirar Khorram Shahr. An bayyana makamin a wani faretin soja da aka gudanar jiya Juma’a a birnin Teheran kuma an ce yana iya cin nisan kilomita dubu biyu, idan an harba shi. Tashar talbijin din kasar ta nuna hotunan gwajin da aka yi. Wani […]

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hankali.

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare […]

Buhari zai ziyarci London daga Amurka

Buhari zai ziyarci London daga Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi izuwa birnin New York dake kasar Amurka domin halartar taron Kwamitin Koli na Majalisar Dinkin Duniya, karo na 72 wanda sauran shuwagabannin duniya zasu halarta. A wata sanarwa da babban mai bawa shugaban kasa shawara a harkar sadarwa, Mista Femi Adesina ya fitar itace shugaban zai halarci tattaunawa ta musamman […]

Ambaliya: Trump na neman dala biliyan 8

Shugaban Amurka Donald Trump na neman dala biliyan 8 domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

Ambaliya: Trump na neman dala biliyan 8

Shugaba Donald Trump na Amurka ya nemi majalisar dokokin kasar ta ba shi kusan dala biliyan 8 a matsayin tallafin da za a taimaka wa wadanda bala’in ambaliya ya shafa a Texas. A wasikar da ke kunshe da wannan bukata wadda aka gabatar ga kakaki majalisar wakilan Amurka, Paul Ryan, darektan kasafin kudi na fadar […]

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

A karo na biyu cikin mako guda, shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania Trump za su sake kai ziyara jihar Texas domin jajintawa mutane da kuma ganewa idununsu yadda guguwar Harvey ta yi barna a yankin.

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

Yayin da yake shirin kai ziyara birnin Houston da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Texas, shugaba Donald Trump ya aika da wasika zuwa majalisar dokokin Amurka, yana neman kusan Dala biliyan 8, wadanda za a yi amfani da su domin tallafawa jihohin Texas da Louisiana. Ana sa ran, wannan bukata da shugaban ya gabatar […]

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Hukumomin Houston a Amurka sun kafa dokar hana fitar dare domin magance matsalar satar kayan jama’a da ake samu sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan agaji.

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Magajin Garin Houston Sylvester Turner ya sanar da kafa dokar hana fitar daren da zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba. Turner ya ce suna da dubban mutanen da suka bar gidajen su domin samun mafaka a sansanonin da aka tanada, amma bata-gari na amfani da damar wajen fasa […]

Donald Trump Na Fuskantar Suka Daga ‘Yan Jam’iyyarsa

Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami'in 'yan sandan jihar Arizona afuwa.

Donald Trump Na Fuskantar Suka Daga ‘Yan Jam’iyyarsa

Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami’in ‘yan sandan jihar Arizona afuwa, bayan da aka same shi da laifin nuna wariya. Kakakin majalisar Wakilan Amurka Paul Ryan ya bayyana cewa, bai goyi bayan shawarar da shugaba Donald Trump ya yanke […]

Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al’umar Texas – Trump

Al'umar jihar Texas da bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa, na ci gaba da samun tabbaci daga hukumomin kasar kan tallafa masu da za a yi domin su koma rayuwarsu ta da yayin da shugaba Donald Trump ya ce har ya fara magana da wasu 'yan majalisar dokokin kasar.

Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al’umar Texas – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin agaza wa mutanen Texas da Louisiana domin ganin sun samu saukin bala’in da ya auka musu na ambaliyar ruwa. Shugaba Trump ya shaidawa taron ‘yan jarida a Fadar White House jiya Litinin cewa wadanda wannan lamari ya rutsa da su, su kwana da sanin cewa za su samu […]

1 2 3 4