Kotu ta bayar da belin Saminu Turaki

Kotu ta bayar da belin Saminu Turaki

Wata kotu a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Saminu Turaki bayan hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin wawure naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulkin jihar. An bayar da belinsa ne bayan wasu mutum biyu mazauna Abuja sun tsaya masa. […]

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu. Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da wani zaman da aka yi a birnin Sakkwato. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyu da suka jagoranci wannan sulhun […]

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

An fara sulhunta wani sabani da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad a Najeriya da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

A ranar Litinin ne dai magajin gari ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin kuma ya sanar da yin Murabus daga kan mukamin wanda ya rike tsawon shekara 20. Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani […]

Ibrahim Magu: ‘A rika daure barayin gwamnati a dajin Sambisa’

Ibrahim Magu: ‘A rika daure barayin gwamnati a dajin Sambisa’

Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya yi kira da a kafa kurkuku a dajin Sambisa domin a rika tsare wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar. Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da ake bikin bude sabon ofishin shiyya na hukumar a Kaduna […]

Ba Wanda Zai Cire Magu – Osinbanjo

Ba Wanda Zai Cire Magu – Osinbanjo

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba wanda zai cire Ibrahim Magu daga mukamin mai rikon Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa tare da yi wa tattalin ariki ta’anti wato EFCC. Mukaddashin Shugaban ya furta hakan ne a wajen bikin bude sabon ofishin hukumar na gunduma a Kaduna. Osinbajo, wanda ya sami wakilcin […]

‘Yan majalisa sun dakatar da nadin mukaman da Osinbajo ya aika

‘Yan majalisa sun dakatar da nadin mukaman da Osinbajo ya aika

Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da sauraron duk wani nadin mukami da bangaren zartarwa ya mika mata, har sai mukaddashin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya janye kalamansa na cewa majalisar na da takaitaccen iko wajen nadin mukamai a kasar. Hakan ya faru ne a zaman da majalisar ta yi a ranar Talata bayan kammala […]

Kotu Taci Tarar Patience Jonathan Naira Dubu Dari Biyar

Kotu Taci Tarar Patience Jonathan Naira Dubu Dari Biyar

Alkali Saliu Seidu na wata babbar kotu dake zaman ta a garin Fatakwal na jihar Rivers a Najeriya ta kallafawa uwar gidan tsohon shugaban Nigeria Dakta Patience Jonathan tarar kudi Naira Dubu Dari Biyar sakamakon janye karar da ta shigar a gaban ta kan hukumar yaki da cin hanci a Najeriya wato EFCC. Ita dai uwar […]

Wani jami’in EFCC ya kubuta a hannun ‘yan bindiga

Wani jami’in EFCC ya kubuta a hannun ‘yan bindiga

Wani babban jami’in Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude masa wuta a birnin Port Harcourt na jihar Rivers. Mista Austin Okwor, wanda jami’i ne ofishin EFCC a Port Harcourt, ya bar ofishin hukumar bayan ya tashi aiki a lokacin […]

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya ce babu wani bambanci tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP a kasar. Sai dai tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ta’annati (EFCC) ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki […]