Ban Mayar Da Osinbajo Saniyar-Ware Ba — Buhari

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da shi saniyar-ware ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.

Ban Mayar Da Osinbajo Saniyar-Ware Ba — Buhari

Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buharin ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan da wata jarida ta ce tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga jinya wasu daga cikin ‘yan fadarsa da suka yi baba-kere sun ware Farfesa Osinbajo inda ba a damawa da shi a harkokin […]

Buhari ya Soke Taron Ministocin na Wannan Makon

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke taron ministoci na wannan mako, wanda shi ne na farko da aka yi tsammanin zai halarta bayan dawowarsa daga jinyar da ya shafe fiye da wata uku yana yi a Birtaniya.

Buhari ya Soke Taron Ministocin na Wannan Makon

Mai ba shi shawara ba musamman kan harkar yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba da safe gabannin lokacin da aka saba fara taron. Ba a dai bayyana dalilin daukar wanan mataki ba, amma dama shugaban yana aiki ne daga gida tun bayan dawowarsa daga […]

Yadda Jonathan ya kassara Najeriya-Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonatahan ta durkusar da Najeriya ta hanyar “Cin hanci da rashawa da kashe kudi ba bisa ka’ida da sauran almundahana”.

Yadda Jonathan ya kassara Najeriya-Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonatahan ta durkusar da Najeriya ta hanyar “Cin hanci da rashawa da kashe kudi ba bisa ka’ida da sauran almundahana”. Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Garba Shehu shi ne ya yi furucin a sanarwar da […]

Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.

Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki. Ya bayyana cewa yana ci gaba da murmurewa da samun koshin lafiya kuma yana bukatar ya dawo gida. “Amma yanzu na […]

Zan koma Nigeria bayan samun yardar likitocina – Buhari

Zan koma Nigeria bayan samun yardar likitocina – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya shafe fiye da wata uku yana jinya a Landan, ya ce yana samun sauki kuma zai koma gida ne kawai idan ya samu amincewar likitocinsa, in ji kakakinsa Malam Garba Shehu. A ranar Asabar ne shugaban ya gana wasu hadimansa a gidan da yake jinya a birnin Landan. Cikin […]

Buhari ya gana da ma’aikatan sa a London

Buhari ya gana da ma’aikatan sa a London

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin jami’an gwamnatin sa ranar Asabar a birnin London dake kasar Birtaniya inda ya shafe fiye da wata uku yana jinya, ya gana da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, mataimakan sa kan harkokin yada labarai Femi Adesina da Mallam Garba Shehu. A cikin tawagar har ila yau, […]

Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan ‘yan gudun hijira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin bayar da agaji saboda "zuzuta" halin da 'yan gudun hijirar da Boko Hara suka kora daga gidajensu ke ciki.

Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan ‘yan gudun hijira

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kungiyoyin suna kambama halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki ne da zummar samun kudi daga wajen gwamnatoci. Ya bayar da sanarwar ce kwanaki kadan bayan majalisar ta dinkin duniya ta ce fiye da mutum 5m da Boko Haram ta raba […]

Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wo gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola ta wayar tarho inda ya yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Saratu Aregbesola.

Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twiiter ta ce Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a London, ya yi wayar ne ranar Alhamis. Ya kara da cewa shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan Saratu Aregbesola. A cewar sanarwar, shugaban na Najeriya […]

An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

A Najeriya, hukumomi sun kori wata kara da aka shigar ana tuhumar wani mutum mai shekara 41, wanda ya sanya wa karen sa sunan Shugaba Muhammadu Buhari. An kama Joachim Iroko, wani dan kasuwa da ake cewa Joe Fortemose Chinakwe, a shekarar 2016, bisa zargin sa da neman tayar da rikici a kasar. Wani alkali […]